Bayan Shekaru 27, Matashi Ya Fara Neman Mahaifinsa Dan Najeriya a Burtaniya, Ya Saki Hoton Auren Iyayensa

Bayan Shekaru 27, Matashi Ya Fara Neman Mahaifinsa Dan Najeriya a Burtaniya, Ya Saki Hoton Auren Iyayensa

  • Shekaru 27 bayan haihuwarsa, wani matashi na neman mahaifinsa wanda ya kasance dan Najeriya
  • A cewar mutumin, an haifi mahaifinsa a kasar Burtaniya sannan ya auri mahaifiyarsa wacce suka hadu a lokacin da yake karatu a cikin shekarun 1990s
  • Ya saki takardar haihuwar mahaifinsa da hoton auren iyayensa a matsayin shaida yayin da ya bayyana cikakkun sunayensu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dan Najeriya, wanda baya so a bayyana sunansa, na ci gaba da neman mahaifinsa dan Najeriya bayan shekaru 27 da haihuwarsa a kasar Burtaniya.

Lauyan Najeriya, Abdulmalik A Othman, wanda ya bayyana neman da matashin ke yi a Facebook, ya saki hotunan takardar haihuwar mahaifin nasa da kuma hoton auren iyayen.

Shi daya tilo iyayensa suka haifa
Wani Mutum a Birtaniya Yana Neman Mahaifinsa Dan Najeriya Bayan Shekaru 27, Ya Saki Hotunan Auren Iyayensa Hoto: Abdulmalik A Othman
Asali: Facebook

A cewar Abdulmalik, an haifi mahaifin matashin a kasar Burtaniya, ya koma Najeriya sannan ya koma inda aka haife shi don yin karatu a shekarun 1990s.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci, Matarsa Da Yara 2, Ciki Harda Jaririn Kwana Daya

A Burtaniya ne ya hadu da mahaifiyarsa sannan ya aureta. Ya ba da sunan mahaifiyar matashin a matsayin Oluyemi Olugbeminiyi Ayoola Funnily Bamidele Gisanrin sannan sunan mahaifinsa Hakeem Adetokunboh Oluwafemi Bamidele Toyosi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da mahaifiyarsa ta kasance ruwa biyu yar Najeriya daga jihar Ogun kuma yar Caribbean daga Barbados, Mahaifinsa dan Lagas ne.

Ma'auratan sun rabu

Abdulmalik ya kara da cewar iyayen mutumin sun rabu sannan mahaifiyarsa ta rasa lambar mahaifinsa tun daga lokacin har yanzu.

An dauki wani mai aikin bincike mai zaman kansa aikin neman mahaifin nasa amma abun ya ci tura. Matashin ya ce mahaifiyarsa bata san inda danginsa suke ba ko kuma hanyar tuntubarsu.

"Ya kuma bayyana cewa mahaifiyarsa Kirista ce a baya kafin ta koma Musulunci saboda soyayyar mahaifinsa.
"Ya ce abu guda da yake da shi shine hoton da aka dauka a wajen daurin auren da kuma wata takardar haihuwa wanda aka hada a kasa. Ya kuma kara da cewar ya biya wani mai bincike mai zaman kansa domin gano inda mahaifinsa yake kuma mahaifiyarsa ta zo Najeriya a 2018 don nemansa amma duk abun ya ci tura," inji wallafar AlbdulMalik.

Kara karanta wannan

Kyau Ya Hadu Da Kyau: Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

Matashin ya yarda cewa mahaifinsa na iya kasancewa a Najeriya. Da aka tuntube shi, Abdulmalik ya tabbatarwa Legit.ng cewa mutum ne kadai iyayensa suka haifa amma bai bayyana sunansa ba.

Jama'a sun yi martani

Joyce Chichi ta ce:

"Wato kenan mahaifiyarsa bata san daga jihar da mijinta yake ba?"

Arákùrin Sodiq Olatunji Oluronbi ya ce:

"Ina rokon Allah ya hada su nan ba da dadewa ba."

Salamatu Ibraheem ta ce:

"Amma yi tunanin wannan abu, kin auri mutum ba tare da ziyartar yan uwansa ba ko sau daya."

Jozie Jozie ya ce:

"Ina rokon Allah ya sa a ji alkhairi."

Yar Najeriya ta samu garabasar N245k a Twitter

A wani labarin, mun ji cewa wata budurwa ƴar Najeriya ta samu sama da N245k a shirin raba kuɗin tallan da aka samu a Twitter wanda Elon Musk ya kawo.

Budurwar mai suna Bamidele, ta sanya hoton ƙididdigar kuɗin da ta cancanci Twitter wacce yanzu aka sani da X, za ta biya ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng