Jerin Ministocin Kudi A Najeriya Tun Daga 1999 Zuwa Yanzu Da Kuma Jihohinsu
‘Yan Najeriya sun zaku su san waye zai karbi ma’aikatar kudi a matsayin minista saboda tasirin ma’aikatar da kuma yadda tattalin arzikin kasar ke tangal-tangal
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Matsayin ministan kudi a Najeriya na da matukar girma da kuma daraja wanda mutane ke mutuntawa saboda tasirin kudade a kasar.
Tun shekarar 1999, gwamnati ta nada ministocin kudi guda takwas da suka hada da Adamu Ciroma da Olusegun Aganga da kuma Ngozi Okonjo-Iweala, Legit.ng ta tattaro.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin ministocin kudi tun 1999 bayan dawowar dimukradiyya a Najeriya.
1. Adamu Ciroma (1999-2003) – Jihar Yobe
Ciroma shi ne gwamnan babban bankin Najeriya, CBN a gwamnatin Murtala Mohammed kafin zama minista a 1999.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kasance a fannin tattalin arziki duk da cewa masanin tarihi ne, daga bisani ya kasance minsitan kamfanoni da kasuwanci.
Ya nemi takarar shugaban kasa har sau biyu a rayuwarsa kafin ya rasu a ranar 5 ga watan Yuli 2018 ya na da shekaru 83.
2. Ngozi Okonjo-Iweala (2003-2006) – Jihar Delta
Ngozi ta kasance masaniyar tattalin arziki da ake tunanin babu kamarta a Nahiyar Afirka gaba daya.
An haife ta a ranar 13 ga watan Yuni a 1954 a Ogwashi-Ukwu da ke jihar Delta, Ngozi ta kasance ministar kudi a gwamnatoci biyu (2003-2006) da kuma (2011-2015).
3. Nenadi Usman (2006-2007) – Jihar Kaduna
Nenadi Esther Usman an haife ta a ranar 12 ga watan Nuwamba 1966 a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, Usman ba ta jima ba a kan kujerar ministan kudi.
An zabe ta a matsayin Sanata daga Kaduna ta Kudu a watan Afrilu na 2011 a tutar jam’iyyar PDP.
4. Shamsudden Usman (2007-2009) – Jihar Kano
Usman ya fara karatunsa ne a King’s College da ke Legas inda daga baya ya wuce jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a jihar Kaduna a fannin tsangayar tattalin arziki.
Shamsudden ya yi aiki a bankuna da dama kafin kasancewarshi ministan kudi a gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar’adua.
5. Mansur Mukhtar (2009-2010) – Jihar Borno
Mansur shi ma ya kasance dalibi daga King’s College kafin daga bisani ya wuce jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a.
Kafin kasancewarshi ministan kudi a gwamnatin marigayi ‘yar Adu’a ya yi aiki a bankuna da dama da sauran hukumomin kudi a Najeriya.
6. Olusegun Aganga (2010-2011) – Jihar Ekiti
An haifi Aganga a ranar 22 ga watan Yuli na 1955, ya kasance masanin tattalin arziki da ya shahara a Najeriya.
A lokacin da ya ke ministan kudi shi ya kawo tsarin fadada tattalin arziki inda kasar ta rage dogaro da man fetur a kasar.
7. Ngozi Okonjo-Iweala (2011-2015) – Jihar Delta
Kasancewarta masaniyar tattalin arziki da kuma kwarewarta shi ya sake bata damar dawowa a matsayin ministar kudin lokacin mulkin Goodluck Ebele Jonathan.
Bayan gwamnatinsu ta kare, an nada Ngozi a matsayin Babbar Darakta a Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) a 2021.
8. Kemi Adeosun (2015-2018) – Jihar Ogun
Adeosun ta rike kujerar minista na shekaru uku kacal bayan cece-kuce a kan takardar shaidar bautar kasa wato NYSC.
A watan Satumba na 2018, Adeosun ta ajiye mukamin ministar kudi saboda cece-kuce da ake ta yi a kan haka.
9. Zainab Ahmed (2018-2023) – Jihar Kaduna
An haifi Zainab a ranar 16 ga watan Yuni na 1960, ta samu shaidar kammala digiri a jami’ar Ahmadu Bello yayin da ta sake yin digiri na biyu a jami’ar jihar Ogun inda ta karanta harkar kasuwanci.
A lokacin da ta ke rike da mukamin ministar kudi, Ahmed ta ba da gudumawa sosai wurin ganin an samu karuwar tattalin arziki a kasar.
Akwai Yiwuwar Ministan Kudi Ya Fito Daga Legas
A wani labarin, ana hasashen shugaban kasa, Bola Tinubu zai iya dauko ministan kudi daga jihar Legas.
Wani babban lauya da ke zaune a Legas, Wale Adeagbo shi ya bayyana haka yayin hira da Legit.ng ta yi da shi.
Asali: Legit.ng