Badaƙalar Naira Biliyan 6.9: Akwai Yiwuwar Emefiele Ya Tafi Gidan Yari Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
- Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele zai gurfana gaban kotu ranar Alhamis mai zuwa
- Zai gurfana ne bisa tuhumar badaƙalar naira biliyan 6.9 da ake ma sa tare da kamfanin wata ma'aikaciyar CBN
- Zai iya fuskantar ɗauri na shekaru biyar kamar yadda sashen na 19 na kundin hukunta laifukan cin hanci ya nuna
FCT, Abuja - A halin da ake ciki, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ka iya fuskantar ƙalubale na ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da samun zaɓin biyan tara ba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya ke ƙarar Emefiele bisa badaƙalar kuɗaɗe har naira biliyan 6.9 kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.
Emefiele zai gurfana a gaban kotu kan badaƙalar naira biliyan 6.9
A ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta ne za a saurari ƙarar da aka shigar da Emefiele a wata babbar kotu da ke zamanta a yankin Maitama da ke Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Emefiele, wata ma'aikaciyar CBN Sa'adatu Yaro da kamfaninta mai suna April1616 Investment Limited, za su gurfana gaban kotu kan tuhume-tuhume guda 20 da ke da alaƙa da badaƙalar kuɗaɗe kamar yadda Channels TV ta wallafa.
Idan za a iya tunawa dai, tsohon gwamnan babban bankin ya kasance a hannun DSS tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi, inda yanzu kuma ake tuhumarsa da badaƙalar waɗannan maƙudan kuɗaɗe.
Mai zai faru idan aka samu Emefiele da laifi
Laifin da ake tuhumar Emefiele ya saɓawa sashe na 19 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka na shekarar 2000.
Idan kotu ta samu gwamnan babban bankin da laifi, za ta yanke ma sa hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.
Wani sashe na kundin yana cewa:
“Duk wani ma'aikacin gwamnati da ya yi amfani da matsayinsa wajen bai wa kansa wata dama ta cin hanci, ko abokin aikinsa, ko kuma wani ma'aikaci daban, ya aikata laifi, kuma zai fuskanci hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zaɓin biyan tara ba.”
Emefiele ya nemi kotu ta ba da belinsa
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan buƙatar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya shigar na neman a ba da belinsa.
Emefiele ya shigar da wannan buƙata ne a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta hannun lauyansa, Joseph Daudu.
Asali: Legit.ng