Kotu Ta Tsare Matashin Da Ya Karya Hannun Budurwarsa Saboda Ta Yi Waya Da Wani Saurayi A Kano
- Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a hukumar Hisbah ta tsare wani matashi kan zargin ji wa budurwarsa ciwo a hannu
- Wanda ake zargin Abbas Sadiq ya karya budurwarsa a hannu bayan ya mata dukan tsiya kan zargin waya da wani mutum
- Alkalin kotun, Khadi Sani Tanimu Hausawa ya ba da umarnin tsare matashin a gidan kaso tare da dage karar zuwa watan Agusta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano – Kotun shari’ar Musulunci a jihar Kano ta tsare wani matashi kan zargin ji wa budurwarsa ciwo a hannu.
Matashin mai suna Abbas Sadiq ya karya hannun budurwarsa kan zargin ta na waya da wani saurayi ba tare da ya sani ba.
Kotun da ke zamanta a hukumar Hisbah na tuhumar Sadiq wanda mazaunin Unguwar Sheka ne a jihar da laifuka har guda uku.
Ma'aikacin JAMB Ya Shiga Tasku Bayan Kama Shi Da Satar Kwamfuta Don Biyan Kudin Haya, Ya Gamu Da Hukuncin Kotu
Me kotun ke tuhumar matashin da shi?
Tuhume-tuhumen sun hada da cin zarafin dan Adam da amfani da karfi sai kuma haddasa rauni ga dan Adam, Politics Nigeria ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jami’an ‘yan sanda sun fada wa kotu cewar budurwarce ta kai musu kara da cewa saurayin ya mata dukan tsiya har sai da ya karya mata hannu.
Ta ce saurayin nata wanda har an saka musu ranar aure ya daka ta ne saboda zargin ta na waya da wani mutum.
Wanda ake zargin ya amsa dukkan tuhume-tuhume da ake a kansa ba tare da wata musu ba, Daily Nigerian ta tattaro.
Wane hukunci kotun ta yanke wa matashin?
Daga nan ne alkalin kotun, Sani Tanimu Hausawa ya bayar da umarnin tsare Sadiq a gidan gyaran hali.
Rahotanni sun tabbaatar da cewa bayan yanke hukuncin, budurwar ta yi dana sani inda ta bukaci magana da saurayin nata da kuma neman su sasanta da juna, cewar Daily Trust.
Daga bisani alkalin kotu ya dage ci gaba da sauraran karar har sai ranar 25 ga watan Agusta na wannan shekara idan Allah ya kaimu.
Kotu Ta Daure Lauyan Bogi A Jihar Kano
A wani labarin, kotun shari'ar Musulunci da ke zamanta a jihar Kano ta tsare wani matashi Zaraddeen San Maidoki kan zargin cin amana da damfara.
Ana zargin matashin da gabatar da kansa a matsayin lauya inda ya yi alkawarin kare wadansu a kotu.
Asali: Legit.ng