Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Hadimin Buhari Ya Bayyana Inda Nasir El-Rufai Ya Koma
- Wani hoton tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana ƴan kwanaki kaɗan bayan bai samu amincewar majalisa ta ya zama minista ba
- Tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya sanya hoton El-Rufai a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 15 ga watan Agusta
- Ahmad ya yi rubutu a saman hoton, inda ya rubuta "Shaƙatawa a Beirut", Beirut shi ne babban birnin ƙasar Lebanon ta yankin Gabas ta Tsakiya
Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana inda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya ke ƴan kwanaki kaɗan bayan majalisar dattawa ta ƙi amincewa ya zama minista.
Ahmad, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter @BashirAhmaad, a ranar Talata, 15 ga watan Agusta, ya sanya hoton Nasir El-Rufai.
Bashir Ahmed ya bayyana inda El-Rufai ya koma
Tsohon hadimin na Buhari ya yi wani rubutu mai cewa "Shaƙatawa a Dubai" a yayin wallafa hoton da ya yi. Birnin Beirut shi ne birni mafi girma a Lebanon kuma shi ne babban birnin ƙasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan ne dai karon farko da ake jin ɗuriyar inda tsohon gwamnan ya koma tun bayan da ya sa ƙafa ya fice daga Najeriya.
Bayan haƙura da zama minista, El-Rufai ya shilla zuwa ƙasar waje
Legit.ng ta rahoto cewa Mallam Nasir El-Rufai ya shilla zuwa ƙasar waje bayan ya haƙura da zama minista a gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Wata majiya mai tushe ta gayawa jaridar Daily Trust cewa, El-Rufai nahiyar Turai zai wuce amma zai fara yada zango ne a ƙasar Masar tukunna.
Kafin ya bar ƙasar, tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ya gana da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
El-Rufai Ya Bada Sunan Wanda Zai Canje Shi a Minista
A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya miƙa sunan wanda zai canje shi domin zama minista a gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
El-Rufai ya miƙa sunan wanda zai canje shi ɗin ne bayan an samu cikas wajen amincewa da shi ya zama minista.
Asali: Legit.ng