Yan Bindiga Sun Sace Mutane Masu Yawa a Jihar Zamfara a Wani Sabon Hari
- Ƴan bindiga sun zo da sabon salo na ɓadda kama wajen aikata mimmunan aikin ta'addanci a jihar Zamfara
- Miyagun ƴan bindigan sun yi shigar mata hada sanya hijabi lokacin da suka kai mummunan hari a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara
- A yayin harin na ƴan bindigan, sun yi awon gaba da mutane masu yawa waɗanɗa ba a san adadin su ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun ɓadda kama cikin shigar mata sun kai farmaki a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da mutane masu yawa.
A cewar rahoton Daily Trust, mazauna garin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kawo farmakin ne da misalin ƙarfe 7:00 na yamma a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta.
Ƴan bindigan waɗanda suka zo a kan babura sun kama harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka tasa ƙeyar mutane masu yawa ciki har da mata da ƙananan yara.
Garin da ƴan bindigan suka farmaka bai wuce tafiyar kilomita 30 ba zuwa ƙaramar hukumar Bungudu inda a ranar Lahadi ƴan bindigan suka sace mutum bakwai ciki har da ɗan sarki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda harin ƴan bindigan ya auku
Wani majiya a garin ya bayyana cewa:
"Ƴan bindigan sun farmaki garin ne ana gama Sallar Maghriba inda suka kama harbe-harbe. Mutane sun riƙa guduwa domin neman tsira inda ƴan bindigan suka riƙa bin su har cikin gidajensu suna tafiya da su."
"Duk da cewa ba a san adadin yawan mutanen da aka sace ba, ƴan bindigan sun tasa ƙeyar aƙalla mutum 50."
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara, CSP Muhammad Shehu, ya ci tura domin bai ɗauki kiran da aka yi masa a waya ba, sannan bai dawo da amsa ba kan saƙon da aka tura masa ta waya har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Matawalle Ya Soki Dauda Kan Rashin Tsaro a Zamfara
A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya soki magajinsa, Dauda Lawal, kam rashin tsaro a jihar.
Matawalle ya zargi Dauda da nuna halin ko in kula kan yadda matsalar tsaron take ƙara taɓarɓarewa a jihar.
Asali: Legit.ng