'Ku Cire Takunkumin Da Ku Ka Kakabawa Nijar’, Dattawan Arewa Sun Fada Wa ECOWAS
- Kungiyar Dattawan Arewa, NEF ta gargadi Shugaba Tinubu kan daukar matakin soji a Nijar
- Shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi shi ya bayyana haka ta bakin kakakin kungiyar, Dakta Hakeem Baba-Ahmed
- Ta ce matakin soji ba zai haifar da ɗa mai ido ba a tsakanin kasashen biyu da suka dade suna tare
FCT, Abuja - Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bukaci Shugaba Tinubu da ECOWAS su cire takunkumi a kan Nijar don samun damar tattaunawa.
Kungiyar ta ce cire takunkumin shi zai ba da damar tattaunawa da kuma dakile yaki a Nahiyar Afirka.
Shugaban taron, Farfesa Ango Abdullahi ya ce dawo da Bazoum da tabbatar da dimokradiyya a Nijar ya zama dole, Vanguard ta tattaro.
Wane gargadi aka ba wa ECOWAS?
Ya ce dole ECOWAS ta bi dukkan hanyoyin kawo maslaha kafin daukar matakin soji a kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abdullahi wanda kakakin kungiyar, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya wakilta ya ce:
"Kariyar Mohamed Bazoum da dawo da dimokradiyya a Nijar ya zama dole.
"Dole sojin Nijar su yi biyayya ga ECOWAS a matsayinsu na wanda su ke karkashinta.
"Ya kamata a fara tattauna batun Bazoum da kuma sojojin mulkin Jamhuriyar Nijar cikin gaggawa."
Wani roko kungiyar ta yi wa ECOWAS?
Ango ya kara da cewa kamar yadda Tribune ta tattaro:
"Tinubu, a matsayinsa na shugaban ECOWAS dole ya samu hanyoyin bin abin a hankali don kada ya yi abin da zai shafi 'yan Najeriya da ke Nijar.
"Kuma ya kamata Najeriya ta cire dukkan takunkumin da ta saka wa Nijar don samun damar tattaunawa."
Abdullahi ya ce amfani da karfin soji a Nijar a zai haifar da ɗa mai ido ba, kuma bai kamata Najeriya su tsunduma a cikin ba.
Kungiyar ta roki 'yan Najeriya da Nijar da kuma shugabanni da kada su yi wani abu da zai ruguza mu'amala mai kyau da kasashen ke da shi shekaru da dama.
Shehu Sani Ya Gargadi Tinubu Kan Daukar Matakin Soji A Nijar
A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan daukar matakin soji a Nijar.
Sani ya ce daukar irin wannan mataki bai kamata a wannan lokaci ba inda ya ce wannan lamari na bukatar sulhu a tsakanin kasashen.
Asali: Legit.ng