FG Za Ta Janye Karar Da Ta Shigar Kan Emefiele Na Mallakar Bindiga

FG Za Ta Janye Karar Da Ta Shigar Kan Emefiele Na Mallakar Bindiga

  • Gwamnatin Tarayya ta na shirin janye korafin mallakar makamai da ake kan dakataccen gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele
  • A ranar Talata, Lauyoyi sun tuntubi babbar kotun Tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas da ta janye tuhuma a kan makamai da ake yi wa Emefiele.
  • An gurfanar da Emefiele kan korafe-korafe da dama da su ka hada da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya na kokarin janye tuhumar da ake yi wa dakataccen gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele na mallakar makamai.

A ranar Talata, Lauyoyi sun tuntubi babbar kotun Tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas da su janye tuhuma a kan makamai da ake yi wa Emefiele.

Gwamnatin Tarayya za ta janye tuhumar mallakar makamai a kan Emefiele
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Janye Karar Da Ta Shigar A Kotu Kan Emefiele. Hoto: @MSIngawa.
Asali: Twitter

A ranar 25 ga watan Juli ne aka gurfanar da Emefiele a gaban kotun Ikoyi da ke Legas kan zargin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Meye gwamnatin ke bukata kan Emefiele?

Yayin sauraran karar, wakilin Gwamnatin Tarayya, Moammed Abubakar ya ce sun yi shirin janye tuhumar da ake wa Emefiele.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubakar ya ce wannan kudiri nasu ya samu goyon baya daga sashi na 174 na kundin tsarin mulkin 1999, cewar Vanguard.

Ya ce bukatar janye tuhumar ta samo asali ne game da wasu abubuwa da ke faman tasowa a karar Emefiele da su ke bukatar kulawa na musamman.

Meye lauyan Emefiele ya ce kan bukatar?

A martaninsa, jagoran lauyoyin Emefiele, Joseph Daudu ya ce babu wannan bukata a gaban kotu.

Ya kara da cewa cire wata tuhuma ko dakatar da ita na wuyan ministan shari'a be kawai na kasa, inda ya ce a yanzu babau ministan shari'a da zai iya aiwatar da hakan, ya kuma dole a yi hakan a rubuce ba a baki ba.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: An Fadawa Tinubu Abu Daya Tak Da Zai Yi Don Shawo Kan Matsalar Tsaro A Jihar Arewa, Ta Nemi Bukata

Mai Shari'a, Oweibo ya ce ya yi mamakin samun wannan batu a gaban kotun, amma zai yi duba akan hakan.

Alkalin kotun ya dage sauraran karar zuwa ranar 17 ga watan Agusta, cewar gidan talabijin na Channels.

DSS Sun Sake Kama Emefiele A Harabar Kotu

A wani labarin, Jami'an hukumar DSS sun sake kama Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN.

Hukumar ta sake kama shi ne bayan samun hatsaniya tsakaninta da hukumar gidajen gyaran hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.