Shehu Sani Ya Bayyana Cibiyar Gwamnati Da Ta Fi Kowacce Zamba a Gwamnatin Buhari

Shehu Sani Ya Bayyana Cibiyar Gwamnati Da Ta Fi Kowacce Zamba a Gwamnatin Buhari

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana CBN a matsayin cibiyar gwamnati da ta fi kowace aikata zamba a karkashin gwamnatin Buhari
  • Tsohon dan majalisar tarayyar ya ce hakan zai kasance ne idan har abun da ya karanta game da babban bankin Najeriya (CBN) ya zamo gaskiya
  • Sani ya nuna kaduwa cewa hakan ya faru ne a karkashin gwamnatin Buhari wanda ya zargi magabatansa da rashin kishin kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon dan majalisar mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cibiyar da ta fi kowace aikata zamba a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sani ya ce babban bankin Najeriya (CBN) shine cibiyar gwamnati mafi damfara a tarihin Najeriya.

Shehu Sani ya ce cbn a karkashin Buhari ta fi kowace cibiyar gwamnati aikata barna
Shehu Sani Ya Bayyana Cibiyar Gwamnati Da Ta Fi Kowacce Zamba a Gwamnatin Buhari Hoto: Muhammadu Buhari/Shehu Sani
Asali: Facebook

Sai dai kuma, ya bayyana cewa hakan zai kasance ne idan har abun da ya karanta game da babban bankin ya zama gaskiya ne.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zauna da Gwamnan CBN Sakamakon Tsinkewar Farashin Dala a Kasuwa

Da yake rubutu a shafinsa na Twitter @ShehuSani, ya yi al'ajabin yadda irin haka zai iya faruwa a karkashin Buhari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya rubuta:

"CBN a karkashin Buhari ita ce cibiyar gwamnati da ta fi kowacce rufa-rufa da aikata zamba a tarihin Najeriya idan har abin da muka karanta shi ne gaskiyar halin da babban bankin yake ciki. Ta yaya hakan ya faru a karkashin wani mutum da ya taba zargin magabatansa da rashin kishin kasa.”

Hakan na zuwa ne bayan wani rahoto ya kawo cewa babban bankin Najeriya na CBN ya ce alawus da aka biya ma’aikata a shekarar 2022 kurum ya haura Naira biliyan 155.63.

Wani labari da The Cable ta fitar ya yi bayanin kudin da babban bankin kasar ya kashe a tsawon shekaru bakwai daga 2016 zuwa 2022.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Bankin ya fitar da rahoton kudin a shafinsa na yanar gizo a karshen makon jiya, kwanaki bayan an ji za a gudanar da bincike a bankin.

Bankin CBN Ya Fadi Abin Da Ya Jawo Naira Ta Sunkuya a Kasuwar Canjin Kudi

A wani labari na daban, babban bankin Najeriya watau CBN ya ta’allaka faduwar Naira da aiko da kudi da ake yi daga kasashen ketare ba tare da hukuma ta sani ba.

An rahoto cewa Gwamnan bankin CBN na rikon kwarya, Folashodun Shonubi ya yi wannan bayani a makarantar tsaro a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng