Jerin Jami’i’o 10 Na Amurka Da ’Yan Najeriya Za Su Iya Yin Karatun Digiri Na Farko Kyauta
- Dalibai daga Najeriya da ma sauran kasashen duniya za su iya samun ilimi kyauta a kasashen waje a halin yanzu
- Baya ga yadda tsadar kudin makaranta, tsadar rayuwa ka iya hana ‘yan kasar karatun jami’a a wannan yanayi
- Mun kawo muku jerin jami’o’in Amurka da kowa zai iya samun gurbin karatu kyauta cikin sauki daga ko’ina a duniya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Karatu ya fara zama kalubale a Najeriya yayin da ake ci gaba da kakaba tsadar kudin makaranta bayan da gwamnati ta fara nemo hanyoyin magance matsalolin kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da sauransu.
A halin da ake ciki a yanzu, akwai wadanda ba za su iya biyan kudin makaranta ba saboda tsadar kudin makaranta da tsadar rayuwa a Najeriya.
Sai dai, akwai kasashen duniya da ke tallafawa mabukata kuma ma su kokari don tabbatar da sun samu ilimi kyauta.
Jami’o’in Amurka 10 da ke ba da ilimi kyauta ga dalibai
Amurka na daga cikin kasashen da ke ba dalibai gurbin karatu tare da daukar nauyin dukkan abubuwan da ake bukata wajen karatu da ma zama a kasar ta Turai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A wannan karon, mun tattaro muku jerin jami’o’i 10 da ke ba da gurbin karatu da da kuma daukar nauyin karatun dalibai daga inda suke a duniya.
Kowacce jami’a daga cikin wadannan 10, suna da abubuwa da suke dubawa wajen daukar dalibai; kama daga kokari a sakandare, bukatuwa, tarihin ahali da cancata bisa ma’aunin da suke dashi.
Ga jerin jami’o’in
Ga su kamar haka, za ku iya duba abubuwan da ake bukata don neman gurbin karatu:
- Jami’ar Boston
- Jami’ar Miami
- Jami’ar Jiha ta San Jose
- Jami’ar Houston
- Jami’ar Chapman
- Jami’ar Simmons
- Jami’ar Michigan
- Jami’ar Gabashin Tennessee
- Jami’ar Duquesne
- Jami’ar California
Karatun ‘yan Najeriya a Saudiyya
A wani labarin, masarautar Saudiyya ta ce zata bada guraben karatu kyauta ga daliban Najeriya 424 don yin karatu a bangarori daban daban a jami'o'in Saudiyya.
A wata sanarwa da ofishin jakadancin Kasar ya fitar a Abuja, ranar Litinin, ta ce guraben na cikin 6,597 da Saudiyya ke bawa daliban Afirka.
Sanarwar ta kuma ce, ana bawa daliban Jamhuriyyar Benin guraben karatu kyauta 150 duk shekara da ma dai sauran kasashen duniya daban-daban.
Asali: Legit.ng