Saudiyya ta bada guraben karatu 424 kyauta ga ɗaliban Najeriya, ta bayyana yadda za a iya samu

Saudiyya ta bada guraben karatu 424 kyauta ga ɗaliban Najeriya, ta bayyana yadda za a iya samu

- Daliban Najeriya 424 zasu amfana da kyautar guraben karatu a jami'o'in Saudiyya daban-daban

- Kasar Benin ita ma zata samu makamancin gurbin karatun guda 150 kyauta daga Saudiyya

- Ofishin jakadancin Saudiyya ya yaba da irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da Najeriya da sauran kasashen Afirka

Masarautar Saudiyya ta ce zata bada guraben karatu kyauta ga daliban Najeriya 424 don yin karatu a bangarori daban daban a jami'o'in Saudiyya.

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Kasar ya fitar a Abuja, ranar Litinin, ta ce guraben na cikin 6,597 da Saudiyya ke bawa daliban Afirka.

Saudiyya ta bawa 'yan Najeriya 424 guraben karo ilimi kyauta, ta bayyana yadda za a iya samu
Saudiyya ta bawa 'yan Najeriya 424 guraben karo ilimi kyauta. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dan ƙwallon Najeriya ya rasu bayan ya yanke jiki ya faɗi a yayin buga wasa a Abeokuta

Sanarwar ta kuma ce, ana bawa daliban Jamhuriyyar Benin guraben karatu kyauta 150 duk shekara.

"Domin sanin hanyar da za a bi da kuma abubuwan da ake bukata don neman gurbin kyautar karatun, dalibai su nemi bayanai daga ma'aikatar harkokin kasashen waje da kuma ma'aikatun ilimin kasashen su.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace ɗaliban ABU Zaria 17 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Za kuma a iya samun bayani daga ofishin jakadancin Kasar Saudiyya.

"Ofishin jakadancin ya kuma yaba da irin kyakkyawar alakar dake tsakanin Saudiyya da Najeriya da kuma sauran kasashen Afirka," a wani bangare na sanarwar.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Amma, kungiyar masu gasa burodi reshen jihar sun bayyana cewa basu goyon harajin.

Wani jigo a kungiyar wanda aka sani da Godfirst ya ce suna shirye shiryen yadda zasu zauna da masu alhakin karbar kudin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164