Wasu Matsafa Sun Sheke Fasto A Cikin Gonarsa Bayan Yin Basaja Cewa Su Leburori Ne A Ondo

Wasu Matsafa Sun Sheke Fasto A Cikin Gonarsa Bayan Yin Basaja Cewa Su Leburori Ne A Ondo

  • Rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo ta kama daya daga cikin matsafan da suka kashe wani Fasto a gonarsa
  • Faston mai suna Dada Itopa ya rasa ransa ne yayin da ya nemi leburori su masa aiki a gona bai san ashe matsafa ba ne
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Funmilayo Odunlami ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce sun kama daya daga cikinsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo – Wasu da ake zargi matsafa ne sun hallaka wani Fasto mai suna Dada Itopa a gonarsa da ke jihar Ondo.

Marigayin mai shekaru 45 ya rasa ransa ne bayan matsafan sun yaudare shi da cewa su leburori ne da za su taya shi aiki a gona.

Matsafa sun hallaka wani Fasto yayin da suka yaudare shi sun leburori ne
Jami'an 'Yan Sanda Sun Cafke Matsafa Da Ake Zargi Da Kashe Wani Fasto A Gona. Hoto: Peoples Gazette.
Asali: Twitter

An kashe Faston ne a gonarsa da ke kauyen Ipele a karamar hukumar Owo na jihar tare da kai wa matarsa farmaki, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Wani Dan Fashi Da Makami Da Aka Kama Ya Ambaci Sunan Sifetan 'Yan Sandan Da Ke Basu Bindigu

Me 'yan sanda suka ce kan matsafan?

Matar mai shekaru 30, Bose Dada ta samu raunuka bayan matsafan sun sassare ta da adduna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Funmilayo Odunlami ta tabbatar da faruwar hakan a ranar Litinin 14 ga watan Agusta.

Ta ce Faston ya nemi taimakon wadanda ake zargin don taimakonsa a gona su yanke masa ciyawu a kan kudi Naira dubu 11, Tori News ta tattaro.

Funmilayo ta kara da cewa daya daga cikinsu mai suna Omatai ya karbi adda a hannun Faston da nufin zai fara aiki a gonar kawai sai ya aika shi lahira.

Shin an kama wasu daga cikin matsafan?

Ta tabbatar cewa an kama daya daga cikinsu mai suna Mohammed Musa yayin da Omatai ya tsere ba a san inda ya ke ba.

Kara karanta wannan

Kyau Ya Hadu Da Kyau: Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

Ta ce:

“Matar ta so ta nemi taimako amma Mohammed ya buga mata sara a kai inda ta samu raunuka kuma yanzu haka ta na asibiti.
“A yayin bincike Musa ya tabbatar cewa sun kai farmakin ne saboda su na bukatar kan mutum don kai wa wani mai maganin gargajiya a Ipele.”

Rundunar ‘yan sandan ta ce ana kokarin kamo wanda ya saka su nemo kayin dan Adam da kuma sauran wadanda ake zargin.

'Yan Sanda Sun Kama Wasu Kan Zargin Satar Mahaifa A Ondo

A wani labarin, 'yan sanda a jihar Ondo sun kama wasu ma'aikatan jinya da satar mahaifa.

Daga cikin wadanda ake zargin akwai mai gadin asibitin da abin ya faru da ya taimaka aka aikata hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.