Nijar: Shehu Sani Ya Bayyana Dalilai 5 Da Suke Jawo Sojoji Ke Juyin Mulki A Afirka Ta Yamma

Nijar: Shehu Sani Ya Bayyana Dalilai 5 Da Suke Jawo Sojoji Ke Juyin Mulki A Afirka Ta Yamma

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana dalilan da suka sa ake yawan juyin mulki a Nahiyar Afirika
  • Sani ya bayyana rashin tsaro da magudin zabe da kuma matsalolin cikin gida da cewa su ne dalilin juyin mulki a Afirka ta Yamma
  • Ya kuma bayyana sauran matsalolin da cewa gwamnatocin sun ruguza martabar dimokradiyya a kasashensu daban-daban

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana abubuwa biyar da ke jawo juyin mulki a Nahiyar Afirka.

Sani ya bayyana haka ne yayin hira da Kamfanin Dillacin Labarai (NAN) a Abuja inda ya nuna rashin jin dadinsa da yawan juyin mulki a Nahiyar musamman Afirka ta Yamma, Legit.ng ta tattaro.

Shehu Sani ya bayyana dalilan da ke sa juyin mulki a Nahiyar Afirka
Sanata Shehu Sani Ya Magantu Kan Dalilan Da Suke Jawo Juyin Mulki A Afirka. Hoto: Janar Tchiani, @Shehu Sani.
Asali: Twitter

Me ke jawo juyin mulkin?

Kara karanta wannan

Kyau Ya Hadu Da Kyau: Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

Ya ce sojojin juyin mulki na yin haka ne saboda an samar musu da kofar yin hakan a kasashe daban-daban na Nahiyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

“Juyin mulki matsala ce ta cikin gida, wanda ba ya faruwa a rana daya, damar aka samar musu shi yasa suke juyin mulki.”

Sani ya jero dalilai biyar da suke haddasa juyin mulki a Nahiyar Afirka musamman Afirka ta Yamma.

Wasu dalilai ne ke jawo juyin mulki?

1. "Na Farko shi ne ruguza martabar dimokradiyya da gwamnatoci suka yi.
2. "Na biyu kuma bambancin da ke tsakanin mutane na arziki, ga tarin talauci a Nahiyar, idan akwai talauci to babu zaman lafiya.
3. "Na uku a cewar sanatan shi ne rashin tsaro a Nahiyar.
4. "Na hudu shi ne babu wani shiryayyen tsari na ceto dimokradiyya a yankin, ya ce da akwai irin wannan tsarin da ba a yi juyin mulki a Nijar ba.

Kara karanta wannan

Sojojin Nijar Sun Fadi Mummunan Abinda Zai Samu Najeriya Da Ba Su Yi Juyin Mulki Ba

5. "Dalili na biyar shi ne matsalolin da aka samu yayin zaben Mohamed Bazoum, kasashe suka zuba ido ba tare da daukar mataki ba."

Juyin Mulkin Nijar: Shehu Sani Ya Yi Magana Kan Matakin Soji

A wani labarin, sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya gargadi Shugaba Bola Tinubu Kan daukar matakin soji a kan Jamhuriyar Nijar kamar yadda kungiyar ECOWAS ta yi niyya.

Sani ya ce ya shawarci Tinubu da ya yi taka tsan-tsan wurin sanin irin matakin da ya kamata ya dauka a kan sojin juyin mulki a Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.