'Yan Sanda Sun Cafke Jami'in NDLEA Dauke Da Miyagun Kwayoyi a Legas

'Yan Sanda Sun Cafke Jami'in NDLEA Dauke Da Miyagun Kwayoyi a Legas

  • Jami'an ƴan sanda a jihar Legas sun cafke wani jami'in hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ɗauke da miyagun ƙwayoyi
  • Jami'an ƴan sandan sun cafke wanda ake zargin ne ɗauke da miyagun ƙwayoyi waɗanda nauyinsu ya kai kilogiram 4
  • Sai dai, rundunar ƴan sandan ba ta tabbatar da cewa wanda ake zargin jami'in NDLEA ne ba kamar yadda ya yi iƙirari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Jami'an ƴan sanda a jihar Legas sun cafke wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi wanda ya yi iƙirarin cewa shi jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Agusta.

A lokacin da aka cafke wanda ake zargin, an same shi ɗauke da ƙwayar 'Marsh-Mallow' mai nauyin kilogiram 4, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Kwadago NLC Da TUC Sun Sha Alwashin Tsunduma Yajin Aiki Idan Aka Kara Farashin Litar Man Fetur

Yan sanda sun cafke jami'in NDLEA
Wasu jami'an NDLEA a bakin aiki Hoto: Newtelegraph.com
Asali: UGC

Wanda ake zargin mai suna Kelechi Chukwumeeije, ya shiga hannun jami'an ƴan sanda ne a ƙarƙashin jagorancin ASP Samuel Sunday.

Wanda ake zargin ya yi iƙirarin shi jami'in NDLEA ne

Wani majiya daga ɓangaren ƴan sandan ya bayyana cewa a binciken farko da aka gudanar, wanda ake zargin ya bayyana sunansa a matsayin Kelechi Chukwumeeije, sannan yana aiki ne a ofishin NDLEA da ke a ƙofar farko ta tsibirin Tin-Can a jihar Legas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyar ya bayyana cewa wanda ake zargin ya bayyana cewa wani na sama da shi ne ya ba shi ƙwayoyin da aka cafke shi da su.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da cafke wanda ake zargin, ya bayyana cewa har yanzu rundunar ba ta tuntuɓi hukumar NDLEA ba domin tabbatar da cewa ko wanda ake zargin jami'in su ne.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki Jihar Arewa, Sun Salwantar Da Rayuka Da Sace Bayin Allah Masu Yawa

Jami'an NDLEA Sun Halaka Mutum 2 a Legas

A wani labarin na daban kuma, jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi sun yi sanadiyyar mutuwar wasu mutum biyu a yayin wani farmaki da suka kai a jihar Legas.

Jami'an na hukumar NDLEA dai sun kai farmaki ne kan wata maɓoyar masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi lokacin da tsautsayi ya ritsa da matasan mutum biyu da aka halaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng