Zauren Tattalin Arzikin Arewa Ya Koka Kan Tafka Asarar N13bn da Aka Yi Bayan Rufe Iyakar Najeriya da Nijar
- A taron da aka gudanar, an bayyana adadin asarar da 'yan kasuwa daga Arewa suka tafka sakamakon juyin mulkin Nijar
- An yiwa Mohamed Bazoum juyin mulki a watan Yuli, lamarin da ya kawo sauyi mai daukar hankali a Afrika
- Ya zuwa yanzu, an bayyana yadda hakan ya fara tasiri kan 'yan kasuwa da masu ruwa da tsakin yankunan
Abuja - Zauren tattalin arziki Arewa (AED), ya bayyana cewa an yui asarar makudan kudade tun bayan da aka garkame iyakar Najeriya da Nijar bayan juyin mulkin soja.
A cewar zauren, akalla an yi asarar kudaden da suka kai N13bn baya ga manyan motocin da ke tsaye a iyakar kasashen biyu da ke jira dauke da kayayyaki masu daraja, rahoton Daily Nigerian.
Wannan na fitowa ne daga bakin shugaban zauren, Ibrahim Shehu Dandakata, inda yace yanzu haka motoci sun fi 2000 a iyakar kasashen biyu.
Yadda 'yan kasuwa suka yi asara
A wani taron manema labarai da zauren ya yi, ya ce yanzu haka 'yan kasuwa sun fara shaida tasirin wannan garkame iyaka da aka yi, New Telegraph ta tattaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar shugaban zauren:
"Kididdiga ta nuna cewa, alakar kasuwanci a hukumance a tsakanin kasashen ya kai $234m (N171bn) yayin da wanda ba a hukumance ba ya kai $683m (N515bn) kuma galibi na kayayyaki masu iya lalacewa."
Alakar Najeriya da Nijar ta Arewa
Hakazalika, ya bayyana adadin mutanen da ke yankin da kuma irin tasirin sauyin da aka samu a kansu da yadda hakan ke kokarin durkusar da kasuwancinsu.
Idan baku manta ba, Nijar dai na makwabtaka ne da jihohin Arewacin Najeriya, ciki har da Katsina da jihar Yobe.
Tun bayan fara batun juyin mulkin Nijar aka fara zaman dar-dar da hango abin da ka iya biyo bayan wannan mummunan labari.
Neman sulhu daga Izala
A bangare guda, fitattun malaman Izala karkashin shugaba Sheikh Bala Lau, sun dira jamhuriyar Nijar a wani mataki na neman hanyar da za ta sa a sasanta lamarin da ya faru na juyin mulki.
A hotunan da Legit.ng Hausa ta gani a shafin Twitter na kafar Zagazola Makama, an ga lokacin da malaman suka sauka a Nijar.
An gano malaman a filin jirgin sama, inda suka samu tarba daga jami’an sojin jamhuriyar ta Nijar da ke makwabataka da Najeriya.
Asali: Legit.ng