Kada Ku Tsoma Baki Tare da Haifar Mana Matsala, Babban Malamin Coci Primate Ya Caccaki Kasashen Turai
- Jagororin juyin mulkin a Jamhuriyar Nijar suna ci gaba da ja bukatur kasashen duniya na barin shugaba Mohamed Bazoum ya dawo kan karagar mulkinsa
- Rashin samun hadin kan wadanda suka yi juyin mulkin ya sa Faransa ka yi Allah wadai da su; A da Nijar ta kasance cikin kasashen yammacin Afirka da Faransa ke da alaka da su
- Da yake magana kamar yadda jama’a da dama suka yi kan Nijar, limamin coci Primate Elijah Ayodele ya shawarci kasashen yammacin duniya da su bi a hankali
Yamai, Jamhuriyar Nijar - Primate Elijah Babatunde Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual da ke Legas a Najeriya, ya bukaci kasashen yammacin duniya da su guji dama lamurra a Jamhuriyar Nijar da aka yi wa juyin mulki kwanan nan.
A cewar Primate Ayodele, "hakan zai kai ga kashe talakawa da hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum".
‘Kada a zubar da jini a Nijar': Primate Ayodele
An bayyana batun Primate Ayodele ne a wani faifan bidiyo da aka uada a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 13 ga watan Agusta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
“Kada ku gwada wata matsala a Nijar. Zubar da digon jini zai kai ga rasa ran shugaban kasar.
"Ya kamata mu warware matsalar Nijar cikin lumana da kwanciyar hankali domin kowa zai nake hannu ya bar jama'a su yi duk abin da suke so."
Matsalar da za ta faru idan aka matsa lamba
Ya ci gaba da cewa:
“Lokacin da kuke shirin haifar da matsaloli ko dama lamura, da gaske za ku haifar da barazana ga rayuwar shugaban kasa.
“Juyin mulkin Nijar ba zai kau ba, kuma duk wanda ke kokarin kawo karfin soja zai haifar da abubuwa da yawa. Kada su kyale irin wannan ya faru.
"Ya kamata mu dauki lamarin cikin sauki kuma mu yi taka-tsan-tsan ta yadda lamarin ba zai kai ga abin da ba mu zata ba."
Izala ta kai ziyarar sulhu Nijar
Fitattun malaman addinin Musulunci karkashin jagorancin shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Bala Lau, sun dira jamhuriyar Nijar a wani mataki na neman hanyar da za ta sa a sasanta lamarin da ya faru na juyin mulki.
A hotunan da Legit.ng Hausa ta gani a shafin Twitter na kafar Zagazola Makama, an ga lokacin da malaman suka sauka a Nijar.
An gano malaman a filin jirgin sama, inda suka samu tarba daga jami’an sojin jamhuriyar ta Nijar da ke makwabataka da Najeriya.
Asali: Legit.ng