Matar da Tsara Haihuwar Jariri 1 Ta Haifi Jarirai 4 Lokaci Guda, Jama’a Sun Yi Martani Mai Daukar Hankali
- Wata mata da ke da tsarin haihuwar daya ta bayyana kaduwa lokacin da ta samu juna biyun jarirai hudu
- Bayan ta haifi yaran, ta dora su akan kujera yayin da mutane da yawa a TikTok suka yaba da kyawunsu
- Wasu masu amfani da kafar sada zumunta sun yi kokarin bayyana mata tasiri da kuma amfanin jariran nata
Wata uwa ta shiga bakin jama’a a kafar yanar gizo, inda ake taya ta murnar haihuwar 'ya'yanta har guda hudu.
Yaran gaba dayansu kamarsu daya kuma kyakkyawa babu laifi. Mahaifiyar ta ce ta kasance tana tsarawa da shirin haihuwar yaro daya ne tak ita da mijinta.
Matar mai suna @rctolver ta ta dora jariran nata akan kujera yayin da take daukar su hoto. A lokacin da ta yada a TikTok, jama'a da dama sun yi murna da sanya albarka.
Wasu mutane sun yi mamaki da hasashen irin fama da aiki tukurun da matar da mijinta za su fuskanta a aikin tarbiyyar yaran.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a a TikTok
Ya zuwa yanzu, mun tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa game da wannan lamarin:
Jermaine Taylor:
"Ya dage hutun shekara sai baba ta gani.”
Tayrenee:
"Zan mayar da uku. Tsadar ta yi yawa.”
angel:
"AWWWWW ‘YAN UUKU.”
HAZEL:
"Su ma kansu suna mamaki kamar yadda kika yi mamaki.”
Nishatrustno1:
"Yaron da ke kusa da yarinyar can tsoho ne.”
kaayy:
"Sun girma abinsu.”
Herban Alchemist:
"Haihuwa daya an gama kenan.”
RaRa Banks:
"Na biyun nan daga hagu tuni ya san halin da ake ciki a rayuwa.”
Yadda wata mata ta haifi 'yan 3
A wani labarin, wasu ma'aurata 'yan Najeriya da aka ambata da suna Mista da Misis Ogeah suna murnar zuwan ‘yan ukunsu bayan shekaru 11 da aure da kuma bari da dama.
Wata 'yar uwarsu, Evelyn Odume, wacce ta ba da wannan labarin mai ban mamaki a ranar Lahadi, 11 ga Afrilu, ta bayyana cewa Allah ya ba shaidan kunya, Yabaleft ta ruwaito.
Shafin Twitter @Naija_PR ma ya yada labarin mai dadi a dandalin sada zumunta, inda jama'a suka bayyana martaninsu mai daukar hankali.
Asali: Legit.ng