Iko sai Allah: 'Yan uku sun auri 'yan uku a rana daya (Hotuna)

Iko sai Allah: 'Yan uku sun auri 'yan uku a rana daya (Hotuna)

- An yi wani biki mai cike da al'ajabi inda 'yan uku suka auri 'yan uku a lokaci guda

- Wannan kasaitaccen biki mai cike da tarihi ya wakana ne a garin Enugu

- 'Yan uku masu suna Kenechukwu, Chinedu da Chukwuebuka sun auri 'yan uku masu suna Okwuoma, Dumalu da Chinwe a rana daya

A wannan zamani, ba abu mai sauki bane ka ga mace ta haifi 'yan uku a lokaci daya. Babban abun mamakin shine ganin 'yan uku sun auri 'yan uku a rana daya.

Wannan al'amarin ya faru a garin Enugu inda 'yan uku suka auri 'yan uku a rana daya a Ngwo.

'Yan uku masu suna Kenechukwu, Chinedu da Chukwuebuka sun auri 'yan uku masu suna Okwuoma, Dumalu da Chinwe a rana daya tattare da 'yan uwa da abokan arziki.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Amaren wadanda basa kama da juna dukkansu sun saka riguna masu kayatarwa launin fari yagin da mazan suka saka kaya iri daya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ga hotunan ma'auratan a kasa:

Iko sai Allah: 'Yan uku sun auri 'yan uku a rana daya (Hotuna)
Iko sai Allah: 'Yan uku sun auri 'yan uku a rana daya Hoto: The Nation
Asali: UGC

Iko sai Allah: 'Yan uku sun auri 'yan uku a rana daya (Hotuna)
Iko sai Allah: 'Yan uku sun auri 'yan uku a rana daya Hoto:The Nation
Asali: UGC

A wani labari na daban, mun ji cewa wani matashi mai shekaru 26 ya tsallaka rijiya da baya a cikin kwanakin karshen mako bayan da ya lalata yarinya mai shekaru bakwai.

Fusatattun mazauna kauyen Akparoji da ke yankin Owukpa na karamar hukumar Ogabdigbo na jihar Benue ne suka yi yunkurin banka masa wuta.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, an kama mutumin mai suna Patrick Onoja Igah yana lalata da yarinya mai shekaru bakwai a farfajiyar coci.

Mazauna yankin sun ce, Ogah wanda aka fi sani da Omolomo, dan asalin Ogwurute Itabono ne a Owukpa. An yi mishi dukan kawo wuka har an kusan kashe shi kafin 'yan banga suka kwace shi tare da mika shi hannun 'yan sanda.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Benue, DSP Catherine Anene, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Trust ta wayar tarho. Ya ce a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun 'yan sanda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel