Mata ta haifi yan uku bayan shekaru 11 da aure da yin bari sau 6

Mata ta haifi yan uku bayan shekaru 11 da aure da yin bari sau 6

- Allah ya azurta wata ‘yar Najeriya da haihuwar yan uku a lokaci daya bayan shekaru 11 da aure da kuma yin bari sau shida

- Yar uwar matar, Evelyn Odume ce ta wallafa kyawawan hotunan uwar da 'yan uku sun, inda ta ce shaidan ya ji kunya

- Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi murna da hakan kuma sun taya ta murnar zuwan jariran

Wasu ma'aurata 'yan Najeriya da aka ambata da suna Mista da Misis Ogeah suna murnar zuwan ‘yan ukunsu bayan shekaru 11 da aure da kuma bari da dama.

Wata 'yar uwarsu, Evelyn Odume, wacce ta ba da wannan labarin mai ban mamaki a ranar Lahadi, 11 ga Afrilu, ta bayyana cewa Allah ya ba shaidan kunya, Yabaleft ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake sace daliban jami'a a Kaduna

Mata ta haifi yan uku bayan shekaru 11 da aure da yin bari sau 6
Mata ta haifi yan uku bayan shekaru 11 da aure da yin bari sau 6 Hoto: Yabaleft
Asali: UGC

Shafin Twitter @Naija_PR ma ya yada labarin mai dadi a dandalin sada zumunta.

@Naija_PR ta rubuta:

"Wata mata 'yar Najeriya ta haifi 'yan uku bayan shekara 11 da aure da kuma "barin ciki sau 6" a jihar Delta."

Da yake maida martani game da labarin mai dadi a shafin Twitter, @ AdekunleBabat11 ya ce:

"Kai !!!! Yesu kana da kyau. Barka Ma! Allah ya albarkaci jariran da sabon Uba da Uwa."

@0lumuyiwac0ker ya ce:

"Kai! Na taya ta murna. A gare ta. Wannan ita ce irin haihuwar da matata ta gaba ke burin samu. Ina taya ku murna, madam."

@IamAyodejii yayi tsokaci:

"Allah ya kasance mai aminci. Ina taya murna."

@SomiL0ve ya rubuta:

"Miji da matar duk sun kasance masu haƙuri da juna. Wannan yana da daɗi."

KU KARANTA KUMA: APC ta ce ba a taba yin gwamnati mai adalci irin ta Buhari ba a tarihin Najeriya

A wani labarin kuma, bayyanar Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a kan babur sanye cikin 'babbar riga' ya haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta.

Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan ya tunawa yan Najeriya da zamanin tsohon gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti.

Fayose, a lokacin da yake mulki, an san shi da wasannin kwaikwayo daban daban wanda ke haifar da martani a shafukan sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel