'Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki a Jihar Plateau, Sun Halaka Mutum 2
- Ƴan bindiga sun kai wani sabon farmaki a jihar Plateau inda suka halaka mutum biyu waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba
- Mutanen da ƴan bindigan suka halaka dai mata ne waɗanda su ke dawowa ɗaga kasuwa bayan sun je neman halal ɗin su
- Sabon harin na zuwa ne ƙasa da sati ɗaya bayan ƴan bindiga sun kai wani hari akan ƴan kasuwa a jihar
Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun sake halaka ƴan kasuwa mutum biyu ƙasa da sati ɗaya bayan sun farmaki ƴan kasuwa a ƙauyen Heipang cikin ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Plateau.
Jaridar The Punch ta tattaro cewa ƴan kasuwan biyu da aka halaka duk mata ne waɗanda ke kan hanyar dawowar su daga ƙauyen Kinat da yammacin ranar Juma'a lokacin da ƴan bindigar suka afka musu.
Da Dumi-Dumi: Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Yi, Sun Bayyana Ranar Dawowa Bakin Aiki
Ƙauyen Kinat yana cikin gundumar Halle a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.
Wani ɗan kasuwa wanda ya tsira a harin na ƴan bindigan, Moses Jat ya tabbatar da halaka matan guda biyu a yayin harin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"Ƴan bindiga sun farmaki wasu mata na ƙauyen Kinat da su ke dawowa daga kasuwa. Sun halaka mutum biyu sannan wasu mutum biyu sun samu raunika."
"Waɗanda suka samu raunikan suna asibiti yanzu haka ana duba lafiyarsu. Amma tambayar a nan ita ce menene mutanen nan suka nema ne da za su farmaki ƴan kasuwa masu dawowa daga kasuwa? Allah ne kawai ya kare wasu daga cikinmu mu ka tsira daga harin."
Ba a samu jin ta bakin hukumomi ba
Kakakin rundunar tsaron da ke wanzar da zaman lafiya a jihar, Kyaftin Oya James, ba a samu jin ta bakinsa ba dangane da lamarin lokacin da aka tuntuɓesa saboda layukan wayarsa a kashe su ke.
Haka kuma, ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, dangane da lamarin ya ci tura saboda bai ɗauki kiran da aka yi masa a waya ba.
'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 17 a Plateau
A eani labarin kuma, ƴan bindiga sun halaka mutum 17 a wani mummunan hari da suka kai a jihar Plateau.
Ƴam bindigan dai sun kai harin ne a cikin tsakar dare inda suka halaka mutanen waɗanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Asali: Legit.ng