Yan Boko Haram Sun Halaka Mutum 5, Sun Yi Garkuwa Da Mata 7 a Jihar Borno

Yan Boko Haram Sun Halaka Mutum 5, Sun Yi Garkuwa Da Mata 7 a Jihar Borno

  • Mayakan Boko Haram sun kashe mutum biyar a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno a ranar Alhamis
  • Majiya ta bayyana cewa yan ta'addan sun kuma yi awon gaba da wasu mata bakwai a yayin harin da suka kai kan ayarin motocin fasinja da na daukar kaya
  • Sai dai kuma, zuwa yanzu rundunar yan sandan jihar ko sauran hukumomin tsaro basu tabbatar da al'amarin ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno - Wasu da ake zaton yan ta'addan Boko Haram ne sun farmaki wasu ayarin motoci dauke da kayayyaki da fasinjoji a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, inda suka kashe mutum biyar da sace mata bakwai, rahoton Ripples Nigeria.

Sun kai hari ne a ranar Alhamis a kan ayarin motocin jami’an tsaro da ke raka motocin fasinja da kayayyaki kusa da garin Banki da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru a karamar hukumar da misalin karfe 2:30 na rana, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sojoji Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Sace Bayan Ajalin 'Yan Bindiga 3, Rundunar Ta Yi Bayani

Yan Boko haram sun farmaki matafiya a jihar Borno
Yan Boko Haram Sun Halaka Mutum 5, Sun Yi Garkuwa Da Mata 7 a Jihar Borno Hoto: The Cable
Asali: UGC

Maharan sun kashe mutum 5 da sace mata 7, majiya

Wata majiya mai tushe da ke tafiya a hanyar Maiduguri-Bama-Banki, mai suna Babagana Kaumi, ya tabbatar da lamarin ga jaridar Punch a wani sakon murya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Ayarin motocin fasinjoji da kaya sun hadu da harin kwanton bauna a kusa da Banki.
"Daya daga cikin motocin ta samu matsala, kuma da hakan ya faru sai gaba daya sojojin su mayar da hankalin a kan motar da ta lalace har sai an gyara ta kafin a ci gaba da tafiyar.
"Abun da ya faru kenan a wannan rana; yayin da sojojin suka mayar da hankalinsu kan motar da ta lalace, sai yan ta'addan suka kai farmaki, inda suka kashe matafiya biyu, direban daya daga cikin motocin da masu taimaka masa biyu sannan suka sace kimanin mata akwai tare da cinnawa motocin wuta."

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Kaumi ya ci gaba da cewa:

"A yan baya-bayan nan, yan ta'addan kan farmaki irin wadannan ayarin moto ci ne inda suke kwace masu kudade da kayan amfani ciki harda takalma masu kyau daga fasinji, sannan sai su kyale su su ci gaba da tafiya ba tare da sun taba su ba, amma a ranar Alhamis da ta gabata, sun kai harin cikin fushi."

Ya ce hare-haren Boko Haram sun kara kamari yanzu a sassan Najeriya da Kamaru na kan iyaka.

Zuwa yanzu hukumomin tsaro basu fitar da wata sanarwa ba.

Tubabbun yan Boko Haram sun shiga hannu a hanyar zuwa Sambisa

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu tubabbun yan Boko Haram da aka mayar garin Bama da ke jihar Borno sun sake shiga hannu kan zargin hada kai da yan ta'adda.

Kamar yadda shafin Zagazola Makama ya rahoto, an kama su ne tare da wasu mutane biyu a hanyarsa ta zuwa dajin Sambisa don haduwa da yan kungiyar ta'addancin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng