Kungiyar Kiristoci Ta CAN Ta Taya Musulmai Jimamin Babban Rashi a Lokacin da Masallaci Ya Rushe a Zaria

Kungiyar Kiristoci Ta CAN Ta Taya Musulmai Jimamin Babban Rashi a Lokacin da Masallaci Ya Rushe a Zaria

  • Kungiyar kiristocin Najeriya ta taya al’ummar Musulmi jimamin abin da ya faru a babban masallacin Zaria
  • An samu aukuwar rugujewar ginin masallaci a Zaria, lamarin da ya jawo mutuwar mutane da yawa a garin
  • Ba wannan ne karon farko da ake samun aukuwar rugujewar gini ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa a wurare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta jajantawa al’ummar musulmi mazauna garin Zaria a jihar Kaduna da ma daukacin al’ummar kasar dangane da mace-mace da jikkatar masallata da aka samu a yayin da masallaci ya ruguje a Zariya.

Idan baku manta ba, a ranar Juma’a ne aka samu samu aukuwar wani iftila’i a Zaria, inda ginin masallaci ya ruso kan masallata, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, a ranar Asabar a Abuja, ya bayyana kaduwarsa game da mutuwar masallatan, tare da yi wa iyalansu ta’aziyya.

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Yadda Masu Rike da Madafan Iko Su ka yi wa El-Rufai Taron Dangi

CAN ta taya musulmai jimami a Zaria
Yadda CAN ta taya musulmai jimamin rushewar masallaci a Zaria | Hoto: @UbaSani
Asali: Twitter

Ta’aziyyar kiristoci ga musulman Najeriya

A kalaman shugaban na CAN:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Muna mika alhininmu da addu’o’inmu ga mutane 25 da suka samu raunuka, muna kuma yi musu addu’ar samun waraka cikin gaggawa.
“Babban masallacin Zaria yana da kimar tarihi da addini, kasancewarsa a tsaye a matsayin muhimmin wurin ibada sama da shekaru 150.”

Daga nan ne ya bayyana jimaminsa tare da taya al’umma alhinin rashin da aka yi na masallata a cikin masallacin mai dogon tarihi.

Ya kamata a dauki mataki

A bangare guda, ya nemi hukumomin da abin ya shafa da hukumar agajin gaggawa su dauki matakin gaggawa wajen ceto wadanda suka makale da wadanda suka tsira da kuma ba su kulawar da ta dace.

Ya kuma bukaci gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da gudanar da cikakken bincike kan musabbabin faruwar lamarin, Channels Tv ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Rufin Masallacin Fadar Sarkin Zazzau Ya Ruftawa Mutane Yayin Da Ake Sallah, An Rasa Rayyuka

A cewarsa, ya kamata gwamnati ta yi bincike da nufin hana sake afkuwar lamarin tare da tabbatar da tsaron lafiyar masallata a duk wuraren ibada a fadin kasar nan.

Yadda masallacin ya ruguje

A tun farko, rahotanni da muke samu daga garin Zaria ta jihar Kaduna shine cewa rufin babban masallacin masarautar zazzau ya ruguzo yayin da al'ummar Musulmi ke tsaka da Sallah.

Kamar yadda sahfin Dokin Karfe TV ta rahoto, lamarin ya afku ne a ranar Juma'a, 11 ga watan Agusta yayin da masallata ke tsaka da Sallar la'asar.

Wani mazaunin unguwar Kaura Zaria mai suna Dahiru Mohammed ya tabbatarwa Legit.ng faruwar al'amarin inda ya ce ginin ya rufta ne a yayin da aka yi raka'a biyu ana na uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.