An ruguje ginin ofishin jakadancin Najeriya a kasar Ghana

An ruguje ginin ofishin jakadancin Najeriya a kasar Ghana

Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai da hare-hare har kashi biyu da aka kai ofishin jakadancin Najeriya da ke Accra, babban birnin Kasar Ghana.

Geoffery Onyeama, ministan harkokin wajen Najeriya, shi ne ya bayyana bakin cikinsa game da hare-haren biyu da wasu mutane da ba a san ko su wa ye ba suka kai ofishin jakadancin kasar.

Rahoton hakan ya fito ne cikin wani sako da ministan harkokin wajen kasar ya wallafa da safiyar ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, a kan shafinsa na dandalin sada zumuta.

Sashen Hausa na jaridar BBC ya ruwaito ministan yana cewa, "muna Allah wadai da wannan hare-hare biyu da masu neman kada a zauna lafiya da ba a san ko su wa ye ba suka kai ofishin jakadancinmu da ke Accra."

Shugaban kasa Buhari, Mataimakinsa; Osinbajo da kuma Ministan Harkokin wajen Najeriya; Geoffery Onyeama
Shugaban kasa Buhari, Mataimakinsa; Osinbajo da kuma Ministan Harkokin wajen Najeriya; Geoffery Onyeama
Asali: Twitter

Ministan ya ce an yi amfani da wata babbar mota da ake yin aikin rusau da ita, wajen ruguje ginin gidaje da ke farfajiyar ofishin jakadancin kasar nan.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta amince da nade-naden Buhari 207 ba tare da ya waiwayi Magu ba

Ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta tattauna da takwararta ta Ghana kan lamarin, inda ta bukaci a yi hanzarin daukan mataki domin bankado miyagun da suka aikata wannan aika-aika.

Kazalika, ministan ya bukaci a tabbatar da ingantaccen tsari kan al'ummar Najeriya da ke zaune a kasar Ghana ta hanyar tsare lafiyarsu da kuma dukiyoyinsu.

A cikin sanarwar da ministan ya fitar, ya kuma yi tsokaci kan shawarar kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta na dakile yaduwar cutar korona.

A bangare daya kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 661 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.29 na daren ranar Asabar 20 ga Yuni na shekarar 2020.

A sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na dandalin sada zumunta na Twitter, ta ce karin karin mutune 661 da suka kamu sun fito daga jihohi 14 na kasar kamar haka;

Lagos(230), Rivers(127), Delta(83), FCT(60), Oyo(51), Edo(31),Bayelsa(27), Kaduna(25), Plateau(13), Ondo(6), Nasarawa(3), Ekiti(2), Kano(2), Borno(1).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel