Chibok: Mai Shekara 13 Da Boko Haram Suka Dauke Ta Dawo Gida Ta Na ‘Yar Shekara 22

Chibok: Mai Shekara 13 Da Boko Haram Suka Dauke Ta Dawo Gida Ta Na ‘Yar Shekara 22

  • Sanata Oluremi Tinubu da Nana Shettima sun hadu da Rebecca Kabu a fadar Aso Rock a Abuja
  • Wannan Baiwar Allah ta na cikin daliban makarantar Chibok da Boko Haram su ka sace a 2014
  • Uwargidar shugaban kasar ta jinjinawa jami’an tsaron da su ka yi nasarar gano dalibar a Kamaru

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Uwargidar shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta karbi Rebecca Kabu a fadar shugaban kasa, bayan shekaru tara da yin awo gaba da ita.

Rebecca Kabu ta na cikin ‘yan matan makarantar garin Chibok da aka dauke a shekarar 2014, Premium Times ta ce an ceto wannan Baiwar Allah.

Tsohuwar dalibar ta samu kyakkyawar tarba a fadar shugaban kasa na Aso Rock Villa, ta na tare da Sanata Remi Tinubu da Nana Shettima a dazu.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Oluremi Tinubu
Oluremi Tinubu, Rebecca Kabu da Nana Shettima Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Tinubu da ta tarbi Rebecca Kabu ta shaida cewa an tabbatar da lafiyarta kuma za ta iya komawa karatu a makaranta a duk lokacin da ta ga ya dace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran 'Yan Chibok za su dawo

Sanata Tinubu ta na mai alwashin gano ragowar ‘yan matan na Chibok da su ke hannun ‘yan ta’addan Boko Haram, ta ce ba a manta da su ba.

Matar shugaban Najeriyar ta yabawa kokarin da Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro (NSA) da hukumar NIA da sauran jami’ai su ka yi.

"Diyarmu, Rebecca, ina yi maki maraba, na dauki dare ina yi maki addu’a, yanzu babu matsala, bayan duk wahalar da su ka faru da ke.
Ba za mu iya bayanin irin yadda mu ka ji da fatar bakinmu ba. Dole a magance ciwon mantuwa, shawo kan shi ya na da wahala sosai.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara ce: Naja’atu Ta Tona Dalilin Shugaba Tinubu Na Tsokano ‘Yaki’ Da Nijar

Rebecca za ta kasance ta farko a jeringiyar wadanda za su dawo, da ita za a fara; ina so in ga ta koma makaranta a lokacin da ta ke so."

- Remi Tinubu

Channels TV ta ce Tinubu ta yi bayanin yadda ta ke amfani da gidauniyarta mai suna Renewed Hope Initiative wajen ganin mata sun samu ilmi.

A Kamaru aka gano Rebecca Kabu

Wani babban jami’in soja, Rear Admiral Yaminu Musa ya ce a ranar 17 ga watan Yuli aka gano Rebecca Kabu a kasar Kamaru bayan jira na shekaru.

A lokacin da aka dauke Kabu a 2014, ta na ‘yan shekara 13 a Duniya, yanzu ta kai 22.

Shugaban IPMAN ya koka

Shugaban ƙungiyar IPMAN ta ƙasa, Chinedu Okoronkwo ya ce su na ganin a tari litar fetur a akalla N750, ya bada uzurinsa ne da tashin Dalar Amurka.

Ana da labari dillalai ba su iya samun dala a bankuna, idan aka je hannun ‘yan canji kuwa $1 ta haura N920 a yau, hakan na nufin fetur zai iya kara tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng