Man Fetur Bai Gama Tashi ba, ‘Yan Kasuwa Sun Hango Karin Farashi a Najeriya
- Dillalan da ke kasuwancin man fetur su na hasashen za a samu karin akalla 10% a kan farashin lita
- Farashin litar man fetur zai tashi ne saboda rashin darajar Naira domin ba a tace danyen mai a gida
- A zahiri yake cewa farashin man fetur zai tashi saboda Dalar Amurka ta na sukuwa kan Naira
Abuja - Farashin litar man fetur zai iya sake tashi kwanan nan zuwa kimanin N750 a hasashen da wasu manyan ‘yan kasuwa su ke yi a Najeriya.
Kungiyar IPMAN ta manyan dillalan mai ta na ganin karyewar da Naira ta ke yi a kan Dala zai jawo canjin farashi, Tribune fitar da rahoton nan.
‘Yan kasuwan sun roki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kawo tsarin da zai rage faduwar Naira, farashin fetur ya na da alaka da kasuwar canji.
Punch ta rahoto kungiyar IPMAN ta na cewa $1 za ta iya kai N1000 idan ba ayi wani yunkuri ba. Tun a jiya aka ji labari an saida Dala a kan N950.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A tanadi karin 10-20%
Mai magana da yawun bakin IPMAN, Chinedu Ukadike ya shaidawa manema labarai cewa alamu sun nuna za a samu karin 10% kan farashin fetur.
Da yake bayani a Abuja, Mista Ukadike ya ce kamfanin NNPC bai canza farashin sari daga N587, da zarar farashin ya canza, gidajen mai za su daga.
Za a samu karin 10% a farashi domin Dala ta na kan N750 ne, yanzu kuwa farashinta ya haura N900
An samu kusan karin 20% a darajar Dala, idan aka yi amfani da wannan, fetur zai zama kusan N750 kenan.
A yanzu farashin Dala a kasuwar canji N910 ne, hakan na nufin kudin fetur da sauran mai za su karu.
Gwamnati ba ta biyan tallafin man fetur, kuma ba a tace danyen mai a Najeriya, da an samu saukin Dala.
- Chinedu Ukadike
Dalar Amurka tayi wuyar samu
BBC Hausa ta ce Chinedu Okoronkwo a matsayinsa na shugaban IPMAN na kasa ya ce farashin man fetur zai tashi idan har Dalar Amurka ba ta sauka ba.
Dillalan mai irin Bashir Dan Mallam sun koka da cewa ba a samun dala da sauki, kullum farashi ya na sake yin gaba ne bayan bankin CBN ya karya Naira.
Meya jawo Dala ta ke tashi?
Tun a yammacin ranar Alhamis ku ka samu labari an rasa gane yadda Dalar Amurka ta ke cigaba da hawa kan Naira a kasuwar canjin Najeriya.
Gwamnan CBN, Folashodun Shonubi ya shaida cewa marasa gaskiya ne su ka shiga harkar BDC domin su rika juya makudan kudi cikin sauki.
Asali: Legit.ng