An Gurfanar Da Fasto A Gaban Kotu Kan Zargin Mallakar Makami Ba Bisa Ka’ida Ba, Bayanai Sun Fito

An Gurfanar Da Fasto A Gaban Kotu Kan Zargin Mallakar Makami Ba Bisa Ka’ida Ba, Bayanai Sun Fito

  • Kotu ta gurfanar da wani shahararren Fasto a birnin Tarayya Abuja kan zargin mallakar makami ba bisa ka’ida ba
  • Wanda ake zargin, Uche Aigbe an taba gano shi ya hau mimbarin majami’a da bindigar kirar AK-47 yayin gabatar da wa’azi
  • Tun farko dan sanda mai gabatar da kara, ACP James Idachaba ya fadawa kotun cewa Uche ya samu bindigar ce daga Sifeta Audu Musa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Kotun majistare da ke zamanta a birnin Tarayya Abuja ta gurfanar da wani Faston majami’ar ‘House of Rock’ Uche Aigbe kan zargin mallakar makami.

An samu bindiga kirar AK-47 a wurin wanda ake zargin mai suna Uche wanda hakan ya sabawa dokar kasa.

An kama Fasto kan mallakar AK-47 a cikin cocin Abuja
Kotun Ta Gurfanar Da Faston Bayan Rike Bindiga Kirar AK-47 A Coci. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Alkalin kotun, Abubakar Isma’il ya yi watsi da korafin Faston inda ya ce ba ta da tushe bare makama, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara ce: Naja’atu Ta Tona Dalilin Shugaba Tinubu Na Tsokano ‘Yaki’ Da Nijar

Meye alkalin kotun ya ce kan wanda ake zargi?

A yayin yanke hukuncin a ranar Alhamis 10 ga watan Agusta kotun majistare da ke Zuba, Alkali Isma’il ya ce dukkan korafe-korafen da ake zargin Uche sun tabbata a kansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jami’an ‘yan sanda tun farko sun zargi Uche Aigbe da Promise Ukachukwu da kuma Olakunle Ogunleye da hadin baki wurin aikata laifuka da mallakar makami ba bisa ka’ida ba, cewar Vanguard.

Sauran korafe-korafen a kansu sun hada da tayar wa mutane hankali da kuma cin zarafin mutane wanda suka musanta zargin da ake musu.

Wa ya gabatar da kara a kotun?

Mai gabatar da kara, ACP James Idachaba ya fadawa kotu cewar wanda ake zargin ya samu makamin ne daga Sifeta Musa Audu da ke ofishin yan sanda na yankin Wuye da aka tura majami’ar tsaro.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Mutum 5 Da Suka Sha Wahala Kafin a Tantance Su a Majalisa

Ya ce aikata hakan ya sabawa sashe na 97 da 114 da kuma 397 na kundin laifuka da hukunci.

Jaridar Punch ta tattaro cewa a ranar 12 ga watan Faburairu an gano Uche Aigbe a kan mimbari dauke da bindiga kirar AK-47 yayin gabatar da wa’azi a majami’ar.

Kotu Ta Daure Mata Kan Cizo A Abuja

A wani labarin, kotun da ke zamanta a Abuja ta daure wata mata da ta ciji mai shago da ta ke musu sulhu yayin da su ke fada da kwastomarta.

Matar da ake zargi mai suna Chioma Okeke da zabgawa Rosemary cizo yayin da ta ke kokarin shiga tsakaninsu a lokacin da su ke fada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.