Khalifa Sanusi Ya Yi Magana Bayan Ya Hadu da Sojojin da Su Ka Yi Juyin Mulki a Nijar
- Malam Muhammadu Sanusi II ya yi wa ‘yan jarida jawabi bayan zamansa da Bola Ahmed Tinubu
- Tsohon Sarkin Kano ya yi kira da a hadu gaba daya domin samun mafita kan rikicin Jamhuriyyar Nijar
- Mai martaba ya na ganin sirrin samun zaman lafiya shi ne a rungumi sulhu, a maimakon karfin tuwo
Abuja - Muhammad Sanusi II ya samu damar ganawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Villa bayan dawowa daga Jamhuriyyar Nijar.
A yammacin Larabar nan, Vanguard ta kawo labari cewa tsohon Sarkin Kano ya na ganin ba gwamnati kadai za a bari da rigimar kasar Nijar ba.
Da ya zanta da ‘yan jarida kamar yadda AIT ta kawo bidiyo, Sanusi ya bada shawarar yadda yake ganin za a shawo kan sha’anin shugabancin.
Muhammad Sanusi II a Aso Rock
Rahoton ya ce Khalifa ya isa fadar ne da kimanin karfe 8:25, yake cewa ya zo ne domin yi wa Mai girma Bola Ahmed Tinubu halin da ake ciki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakan ya na zuwa bayan ziyarar da Mai Martaban ya kai zuwa kasar makwabtan a yau dinnan, kwanaki kadan da karewar wa'adin da aka bada.
Halifan Tijjaniyyah na Najeriya ya yi tafiyar ne a lokacin da aka rufe sararin samaniyar Nijar a lokacin da ake makawa kasar takunkumi.
"No zo ne in kyankyasa masa bayanin tattaunawa ta da shugabannin kasar Jamhuriyyar Nijar.
Za mu cigaba da yin bakin kokarinmu na jawo bangarorin biyu domin a kara samun fahimta. Yanzu lokacin da jama’a za su bi diflomasiyya ne
Ba lamari ne da za a bar wa gwamnatoci ba, duka ‘Yan Najeriya, duka ‘Yan Nijar su na bukatar su hadu domin a nemawa Afrika mafita
Sai an samu mafitar da za tayi wa Nijar aiki kuma tayi wa Najeriya aiki, sannan ta yi wa Bil Adama.
- Muhammad Sanusi II
Wanene ya tura Sanusi II zuwa Nijar?
Da aka tambaye shi game da wanda ya tura shi wannan aiki, Sanusi II ya tabbatar da ba gwamnati ta aika shi ba, amma ta san da zuwan shi kasar.
"Ba gwamnati ta aika ni ba. Jami’an gwamnati sun san zan je, amma zabin kai na ne, na yi amfani da mutane na, aiki na ne a matsayi na shugaba."
- Muhammad Sanusi II
Yunkurin Muhammadu Sanusi II
A yau aka ji yadda Malam Muhammadu Sanusi II da Shugaban mulkin soja na Jamhuriyar Nijar su ka hadu a babban birnin kasar na Niamey.
Sarkin Kano na 14 zai sa ran yin abin da Sarkin Musulmi da Janar Abdussalami Abubakar su ka gaza a matsayin wakilan kungiyar ECOWAS.
Asali: Legit.ng