Hambararren Shugaban Nijar, Bazoum Ya Ce Busasshiyar Shinkafa Kawai Ake Ba Shi A Inda Aka Killace Shi

Hambararren Shugaban Nijar, Bazoum Ya Ce Busasshiyar Shinkafa Kawai Ake Ba Shi A Inda Aka Killace Shi

  • Hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya koka kan yadda sojoji ke kuntata masa
  • Bazoum ya ce duk abincin da suka ba shi ya rube, yanzu gayar shinkafa ya ke ci da taliya
  • An kifar da gwamnatin Bazoum ne a ranar 26 ga watan Yuli inda sojojin su ka rusa kundin tsarin mulkin kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yamai, Nijar – Hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya bayyana yadda aka killace shi tare da ba shi busasshiyar shinkafa da rashin kulawa na magani.

Sojoji sun kifar da gwamnatin Bazoum ne a ranar 26 ga wata Yuli tare da rusa dukkan hukumomni gwamnati da kundin tsarin mulkin kasar.

Bazoum ya koka kan irin gayar shinkafa da sojoji su ke ba shi
Hambararren Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum Ya Bayyana Irin Halin Da Ya Ke Ciki. Hoto: CNN.
Asali: Facebook

Meye Bazoum ya ce game da killace shi?

Daily Trust ta tattaro Bazoum na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano Sanusi II Ya Zauna Da Sojojin Da Suka Kifar Da Bazoum a Nijar

“An hana ni mu’amala da mutane tun ranar Juma’a, babu wanda ya ke kawo min abinci ko magani.”

Bazoum ya ce ya na rayuwa ba tare da wutar lantarki ba fiye da mako daya, wannan ta shafi ko wane dan kasar bayan Najeriya ta yanke wutar da ta ke ba su.

Ya kara da cewa duk nau'in abinci da ake ba shi sun rube, yanzu ya koma cin gayar taliya da shinkafa, cewar CNN.

Ya na samun damar magana da mutane?

Duk da killace shi da aka yi, Bazoum ya samu damar magana da mutane, duk da an hana shi magana da mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland.

Hakan ya faru ne bayan Nuland ta ziyarci Yamai, amma Bazoum ya samu damar yin magana da sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken a waya.

Tun bayan hambarar da Bazoum, Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS ke kokarin amfani da karfin soji a kan kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da El-Rufai Da Wike a Gidan Gwamnati

Tun farko kungiyar sun ba wa sojojin wa'adin mako daya da su yi gaggawar mika mulki ga Bazoum, amma sojin sun yi biris.

ECOWAS: Dakarun Mali Da Burkina Faso Dira A Jamhuriyar Nijar? Bayanai Sun Fito

A wani labarin, sojojin kasashen Mali da Burkina Faso sun dira a Jamhuriyar Nijar don taimakawa sojin kasar.

Rahotanni sun tabbatar da hakan bayan hukumar yada labarai da hulda da jama'a ta kasar ta wallafa hotunan sojojin Mali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.