Jerin Kasashen Nahiyar Afirka 10 Da Suka Fi Siyan Man Fetur Da Tsada A 2023

Jerin Kasashen Nahiyar Afirka 10 Da Suka Fi Siyan Man Fetur Da Tsada A 2023

  • Bola Tinubu ya cire tallafin mai a ranar 29 ga watan Mayu yayin karbar rantsuwar kama mulki a Abuja
  • Tun bayan cire tallafin, 'yan Najeriya ke fama da tsadar man fetur da ya haddasa raguwar amfani da man a kasar baki daya
  • Ganin yadda man ke da alaka da duk fannonin hada-hada na rayuwa, hakan ya kawo tashin farashin kayayyaki a kasar baki daya

FCT, Abuja - Tun bayan cire tallafin man fetur a Najeriya, 'yan kasar ke fama da hauhawan farashin kayayyaki.

Kamar sauran kasashe, tattalin arzikin Afirka na tangal-tangal saboda tashin farashin mai da ya addabi jama'a.

Kasashen da su ka fi tsadar man fetur 10 a Nahiyar Afirka
An Fitar Da Rahoton Kasashe 10 Da Suka Fi Siyan Man Fetur Da Tsada A 2023. Hoto: Pulse.
Asali: Facebook

Man fetur na da tasiri matuka kan hada-hadar kasuwanci da sufuri da kamfanoni da sauransu, Pulse ta tattaro.

Kasashen Afirka na cikin matsi na tsadar man fetur

Kara karanta wannan

Farashin Litar Man Fetur Zata Faɗi Warwas Ta Dawo Ƙasa da N200 a Najeriya Idan Aka Yi Abu 1

Kasashen Nahiyar Afirka sun fi samun matsalolin tattalin arziki da ya shafi man fetur idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya, cewar Business Insider Africa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saboda tashin farashin mai a kasashen Afirka, wasu daga cikinsu sun yi ta zanga-zanga don kalubalantar gwamnatoci kan farashin mai din.

A Najeriya, bayan Bola Tinubu ya cire tallafin man, mutane sun shiga mayuyacin hali na matsin tattalin arziki da tsadar man fetur.

Tsadar mai a kasar na da alaka da tashin farashin kaya ganin yadda komai ba ya tafiya ba tare da man fetur din ba.

Jerin kasashen Afirka da suka fi siyan man fetur da tsada a 2023

Farashin ko wane lita a jerin kasashe goma na Nahiyar Afirka:

1. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya - N1,400

2. Malawi - N1,260

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

3. Senegal - N1,259

4. Zimbabwe - N1,193

5. Seychelles - N1,175

6. Mauritius - N1,160

7. Morocco - N1,155

8. Cape Verde - N1,110

9. Mali - N1,101

10. Burkina Faso - N1,081

Cire Tallafi: Karyewar Farashi, Rashin Ciniki Da Sauran Matsalolin Da Suka Addabi Masu Gidajen Mai

A wani labarin, tun bayan cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi, 'yan Najeriya na cikin mayuyacin hali da tashin farashin kaya.

'Yan Najeriya sun shiga mawuyacin hali tare da tsadar kayayyaki da ya ke neman ruguza musu harkokin kasuwanci.

Masu gidajen mai a kasar su ma sun bayyana irin matsin da su ke ciki tare da bayyana cewa su na daf da samun matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.