Hukumar Kwastam Ta Zayyano Sharuddan Buɗe Iyakoki Domin Ci Gaba Da Shigo Da Motoci, Shinkafa, Da Sauransu
- Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), ta bayyana sharuddan da za a cika kafin buɗe iyakokin Najeriya
- Shugaban hukumar na wucin gadi Bashir Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan da yake jawabi ga al'ummar kan iyakoki
- Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta buɗe iyakokin da zarar an samu cikakken tsaro da zaman lafiya a Najeriya
Ogun - Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Bashir Adewale Adeniyi, ya lissafo sharuɗɗan sake bude iyakokin kasar nan.
Bashir ya ce akwai wasu dokoki da hukumar za ta waiwaya ta ga ko ana binsu da kyau ko akasin hakan.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wata ziyara ga a ofishin hukumar da ke kan iyakar Idiroko da ke jihar Ogun kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta kwastam za ta yi wa wasu dokoki garambawul
Daga cikin abubuwan da hukumar ta kwastam take so a duba akwai batun siyar da mai a gidajen man da ba su wauce kilomita 20 ba tsakaninsu da bakin iyakokin ƙasa.
Ya ce hukumar ta kwastam za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an ragewa wasu daga cikin dokokin tsauri.
Ya ce akwai wasu dokokin da wasu hukumomin na Gwamnatin Tarayya da ke aiki a kan iyakokin ne suka sanya su.
Bashir ya bayyana sharaɗin bude iyakokin Najeriya
Bashir Adewale ya kuma ce bude iyakokin domin a ci gaba da shigo da kayayyaki da suka haɗa da shinkafa da motoci, ya ta'allaka ne ga haɗin kan da mazauna iyakokin suka ba gwamnati.
A wata ziyara da ya kai a 'Seme Border' da ke Badagry ta jihar Legas, bashir ya buƙaci mazauna kan iyakokin su taimakawa jami'an tsaro da bayanai na sirri kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta buɗe iyakoki da zarar an samu haɗin kan jama'a sannan kuma aka ga cewa an samu sauƙin matsalolin tsaro a Najeriya.
Bashir ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a sake duba takunkumin da aka sanyawa gidajen mai saboda cire tallafin da aka yi.
Hukumar kwastam ta yi ƙarin haske kan dalilin rufe iyakokin Najeriya da Nijar
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan dalilin da hukumar kwastam ta bayar na rufe iyakokin Najeriya da Nijar.
Hukumar ta ce rufe iyakokin da aka yi ba shirin yaƙi ba ne da jamhuriyar ta Nijar, cikin umarni ne kawai na kungiyar ECOWAS da Tinubu ke jagoranta.
Asali: Legit.ng