Sultan, Fastoci Sun Gargadi Tinubu Da ECOWAS Kan Shirin Tura Soji Nijar, Sun Bayyana Matsayarsu

Sultan, Fastoci Sun Gargadi Tinubu Da ECOWAS Kan Shirin Tura Soji Nijar, Sun Bayyana Matsayarsu

  • Kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta yi fatali da shirin afkawa Jamhuriyar Nijar da yaki da ECOWAS ke shirin yi
  • Har ila yau, kungiyar limaman majami'u ta soki shirin kungiyar ECOWAS na amfani da karfin soji a Nijar
  • Dukkan kungiyoyin biyu sun roki Shugaba Tinubu da ya dakatar da kasashen ECOWAS kan wannan kudiri na su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ana ta samun korafe-korafe kan shirin kasashen ECOWAS na afkawa Jamhuriyar Nijar da yaki tun bayan sanarwar da kungiyar ta yi.

Kungiyar Gamayyar Limaman Majami'u (CBCN) da Jama'atul Nasril Islam (JNI) sun caccaki Bola Tinubu kan wannan kudiri na su da ECOWAS.

Sultan da Fastoci sun gargadi ECOWAS kan tura dakarun soji Nijar
JNI DA Kungiyar Limaman Coci Sun Gargadi Kasashen ECOWAS Kan Shirin Amfani Da Karfin Soji A Nijar. Hoto: ECOWAS.int.
Asali: Facebook

Sakataren kungiyar Nasril Islam, Farfesa Khalid Aliyu ya bayyana rashin jin dadinsu kan juyin mulki a Nijar amma ya yi gargadi kan daukar matakin soji da ECOWAS ta shirya yi, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Mun fi karfinku: Jigon APC ya gargadi sojojin Mali, Nijar da suke barazanar taran na Najeriya

Farfesan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a ranar Asabar 5 ga watan Agusta a Kaduna inda ya ce sun yarda da dimukradiyya wurin tabbatar da adalci da aiki da doka, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Mun yarda dimukradiyya na kawo ci gaba da tabbatar da aiki da doka a kasa.
"Babu tantama, dimukradiyya na hana amfani da karfi wurin aiwatar da abubuwa da bayar da daman 'yancin ko wane dan Adam.
"Har ila yau, muna kira da babbar murya, gwamnati ta guji yin amfani da karfin soji a kan kasar Nijar.
"Tattaunawa da sulhu shi ne babban makamin kawo zaman lafiya a yankunan Sahel."

A na sa bangaren, shugaban kungiyar limaman majami'u, Rabaran Lucius Iwejuru ya gargadi Bola Tinubu kan amfani da karfin soji a kan Nijar, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ahir dinka: PDP ta ja kunnen Tinubu, ta ce kada ma ya fara yakar Nijar, ga dalili

Iwejuru ya ce:

"Makon da ya gabata, kungiyar ECOWAS ta yi wata ganawa a Abuja inda ta tattauna batun juyin mulki a Nijar tare da ba su mako guda don dawo da dimukradiyya.
"Mu na kira ga Shugaba Tinubu ya janye wannan kudiri na amfani da karfin soji a kasar, an zubar da jini a Najeriya da Nahiyar Afirka, ya isa haka.
"Mu sani cewa ba a gyara barna da barna, ya kamata a kaucewa duk abin da zai kawo zubar da jini.

Juyin Mulkin Nijar: Shugaba Tinubu Ya Samu Sabon Gargadi Kan Shirin ECOWAS Na Tura Dakaru

A wani labarin, an gargadi Shugaba Bola Tinubu kan amfani da karfin soji a Nijar kamar yadda kuniyar ECOWAS ke shirin yi.

Babban lauya a Najeriya, Femi Falana shi ya yi wannan gargadi a ranar Talata 2 ga watan Agusta a Legas.

Falana ya ce tun da sojoji da suka kwace mulki ba za su mika mulki ba, ECOWAS ta sanya musu takunkumi masu tsauri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.