Jerin Jihohin Najeriya da Suka Hada Iyaka da Jamhuriyar Nijar
- Ƙungiyar bunkasa tattalin arziƙin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) na shirin sanya takunkumi kan jamhuriyar Nijar bayan juyin mulki
- Sojojin sun sanar da Abdrahmane Tchiani a matsayin sabon shugaban ƙasa na mulkin soja bayan kifar da gwamnatin Muhammed Bazoum
- Jihohin arewa 7 sun haɗa iyaka mai tsawon kilomita 1,600 yayin da shiyyoyi Bakwai suka haɗu da Jamhuriyar Nijar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wasu daga cikin jihohin Najeriya sun haɗa iyaka da Jamhuriyar Nijar kuma ana fargabar rikici ka iya shafarsu idan ƙungiyar ECOWAS ta aiwatar da shirinta na ɗaukar matakin soji.
Ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin kasashen yammacin nahiyar Afirka (ECOWAS) ita ce uwa ga ƙasashen Afirka ta yamma.
Shugabannin ECOWAS sun amince da tura dakarun soji Nijar matuƙar jagororin da suka jagoranci juyin mulki ba su haƙura sun maida mulki hannun farar hula ba zuwa ranar 6 ga watan Agusta.
Tuni wasu 'yan Najeriya suka fara kallon wannan shiri na daukar matakin sojin da mafarin yaƙi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane jihohi ne suka haɗa iyaka da Jamhuriyar Nijar?
Sannannen ɗan jaridar nan ɗan asalin Najeriya daga jihar Kano da ke zama a ƙasar waje, Ja'afar Ja'afar, ya bayyana yawan jihohin da suka haɗa boda na Nijar a shafinsa na Tuwita.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku jihohin da suka haɗa boda da Nijar, ga su kamar haka:
1. Jihar Sakkwato
Jihar Sakkwato na cikin shiyyar Arewa Maso Yamma kuma ta haɗa iyaka da Jamhuriyar Nijar. Jihar na kusa da Kogin Sokoto da kuma Kogin Rima. A 2005, jihar na ƙunshe da mutane 4.2m.
Kasancewarta jihar Shehu, Musulmai ne suka mamaye birnin kuma a nan ne kujerar shugaban Musulmai lamba ɗaya take watau Sarkin Musulmai (Sultan).
2. Jihar Kebbi
Kebbi na ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya, ta haɗa iyaka da jihar Sakkwata a gabashi, iyaka da Zamfara a Arewaci da kuma Neja a Kudanci.
Amma a yammacin jihar Kebbi kuma ta haɗa iyakoki da Jamhuriyar Benin da kuma Jamhuriyar Nijar. A cikin jihohi 36, Kebbi ce ta 10 a girma kuma ta 22 a yawan jama'a.
3. Jihar Katsina
Itama Katsina tana cikin shiyyar Arewa maso Yamma, ta haɗa iyakoki da jihohin Kaduna, Zamfara, Kano da Jigawa. Ana mata laƙabi da 'Ɗakin kara'.
Manyan birane biyu Katsina da Daura, ana kallonsu a matsayin cibiyar addinin Musulunci da ilimi a Najeriya.
4. Jihar Zamfara
Kamar dai sauran jihohin da muka ambata a sama, jihar Zamfara na cikin shiyyar Arewa maso Yamma, kuma babbar birninta shi ne Gusau, sannan sunan gwamna mai ci, Dauda Lawal.
Har zuwa shekarar 1996, baki ɗaya jihar Zamfara na cikin jihar Sakkwato.
Sheikh Rijiyar Lemu Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci Ga Shugaba Tinubu Kan Tura Sojoji Jamhuriyar Nijar
5. Jihar Jigawa
A ranar 27 ga watan Agusta, 1991 aka kafa jihar Jigawa lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Ibrahim Badamasi Babangida, jihar tana cikin shiyyar Arewa maso Yamma.
Jigawa ta haɗa iyaka da babbar bodar Najeriya mai iyaka da jamhuriyar Nijar.
6. Jihar Yobe
Yobe na shiyyar Arewa maso Gabas, ta fi shahara da jihar Noma, an kirkiro jihar ranar 27 ga watan Agusta, 1991. Daga cikin jihar Borno aka fitar da Yobe.
Damaturu ne babban birnin jihar Yobe yayin da gari mafi girma da yawan al'umma a kafatanin jihar shi ne Potiskum.
7. Jihar Borno
Borno na ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya, ta haɗa boda da Yobe a Yammaci, Gombe a Kudu maso gabashi da kuma Adamawa a kudanci.
A gabashin jihar Borno kuma akwai babbar bodar Najeriya da ƙasar Kamaru, Arewacin jihar kuma babbar bodar ƙasa da Jamhuriyar Nijar, sai kuma Kudu maso Gabas ta haɗa iyaka da Chadi.
Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙo Ga Majalisa, Ya Faɗi Shirin Tura Sojoji Nijar da Wasu Matakai da Zasu Ɗauka
Jihar Borno ce jiha ɗaya tilo a Najeriya da ta haɗa manyan iyakokin ƙasashe guda uku.
Hambararren Shugban Nijar Ya Roki Amurka da Wasu Kasase Su Kai Masa Ɗauki
A wani rahoton kuma Muhammed Bazoum, shugaban Nijar da sojoji suka kifar ya aike da sako ga Amurka da sauran ƙasashen duniya.
shugaban Nijar wanda ya rasa kujerarsa makon da ya gabata, ya ce yana rubuta wannan sakon ne a matsayin wanda ke tsare.
Asali: Legit.ng