An Ƙwaƙwulo Cin Mutuncin da Mai Shirin Zama Minista Ya yi wa Buhari a 2020
- Bosun Tijjani ya shiga sahun karshe na mutanen da ake sa ran su zama sababbin Ministocin tarayya
- Masanin kimiyyan ya rika sakin baki a baya, yana sukar gwamnatin APC da wasu shugabanninta
- Alamu sun nuna Dr. Tijjani ya na goyon bayan Peter, wannan bai hana Bola Tinubu ya dauko shi ba
Abuja - Bosun Tijjani ya na cikin wadanda Bola Ahmed Tinubu ya aika sunansu zuwa majalisar dattawa domin su zama Ministocin tarayya.
Abin da ya bada mamaki shi ne yadda tun jiya aka rika lalubo wasu maganganu da Dr. Bosun Tijjan ya rika yi kafin zuwan rana irin ta yau.
Idan aka duba abubuwan da masanin kimiyyar ya rika fada a shafinsa na Twitter, za a fahimci ya yi ta sukar gwamnatin APC a shekarun baya.
Bosun Tijani a dandalin Twitter
Tijjani mai Mabiya fiye da 40, 000 yanzu a dandalin sada zumuntan ya taba kai korafi ga majalisar Birtaniya da ta kakabawa Najeriya takunkumi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan mutumi ya yi wannan kira ne a lokacin da ake gwagwarmyar EndSARS a 2020.
A wasu lokutan kuma, Legit.ng Hausa ta gano Tijjani ya na sukar Atiku Abubukar, ya ce kyau ‘dan takaran na PDP ya marawa Peter Obi baya a 2019.
Tijani ya yi wa Buhari kaca-kaca
Abin da ya fi daukar hankali shi ne lokacin da Tijjani ya yi kaca-kaca da Muhammadu Buhari a Afrilun 2020 da yake shugaban kasa.
"Maza da mata masu gaskiya da ke tare Buhari su taimaka mana, mu gane abin da ya sa za su mika rayuwarsu ga mara lafiyan da bai san halin da ake cigaba, ya mulki Najeriya.
Su yi mana bayanin yadda Buhari ya cancanta ya jagoranci kasa irin Najeriya. Ayi mana bayani.
Yin bakin kokari domin ganin Muhammadu Buhari ya tsaya a kan mulki cin amanar kasa ne a ra’ayina kuma ya nuna mutum bai da gaskiya.
Mutane da-dama su na kokawa a Najeriya kuma za su iya mulki. Idan ka yi sanadiyyar hana a samu zabi na kwarai, kai makiyi ne."
- Bosun Tijjani
Bashir Ahmaad ya yi martani
Da yake maidawa wani amsa a wannan dare, Tijjani ya ce bai dace Muhammadu Buhari ya rike ko da shugaban karamar hukuma a Najeriya ba.
Hakan ya jawo Bashir Ahmaad ya yi raddi, ya ce sai ya magance duka matsalolin da ake fama da su da zarar ya shiga FEC tun da shi ya na da lafiya.
Za a rasa shugabanni 5 a Majalisar NWC
Bayan tafiyar Sanata Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore, wasu sun bar Jam’iyyar APC, dazu aka ji labari jigo a APC mai-mulki ya ajiye kujerarsa.
Ahmed El-Marzuk wanda ya fito daga Katsina, ya bar ofishinsa na Mai bada shawara a kan shari’a, zuwa yanzu ba a ji wanda ya maye gurbin na sa ba.
Asali: Legit.ng