Sojoji Sun Halaka Gawurtattun Shugabannin Yan Bindiga Ado Aliero Da Dankarami A Zamfara

Sojoji Sun Halaka Gawurtattun Shugabannin Yan Bindiga Ado Aliero Da Dankarami A Zamfara

  • Rundunar sojin sama a Najeriya ta hallaka gawurtattun 'yan bindiga biyu bayan luguden wuta a jihar Zamfara
  • Gawurtattun shugabannin mayakan sun hada da Ado Aliero da kuma Dankarami da ke karamar hukumar Zurmi
  • Rundunar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa ta bakin kakakinta, Edward Gabkwet

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Rundunar sojin sama ta hallaka wasu jiga-jigan 'yan bindiga yayin luguden wuta daga sama a jihar Zamfara.

Yayin luguden wutan, rundunar ta yi nasarar hallaka wasu 'yan bindigan 10 da suka addabi yankunan Arewa maso Yamma.

Sojin sama sun hallaka gawurtattun shugabannin 'yan bindiga a Zamfara
Rundunar Sojin Sama Ta Halaka Gawurtattun Shugabannin Yan Bindiga A Jihar Zamfara. Hoto: Security Digest.
Source: UGC

Daily Trust ta bayyana sunayen 'yan bindigan da aka hallaka da Ado Aliero da Dankarami.

Yadda sojin su ka yi wa 'yan bindigan luguden wuta daga sama

A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce jami'ansu sun kara kaimi wurin kakkabe 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Assha: Yadda 'yan Arewa suka tafka asarar N13bn saboda abin da su Tinubu suka yi a Nijar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Cewar sanarwar:

"A kokarinta na kakkabe 'yan bindiga da ayyukansu a yankin Arewa maso Yamma, rundunar ta kara kaimi a wani samame da ta kai tsakanin 28 zuwa 29 ga watan Yuli.
"Rundunar 'Operation Hadarin Daji ta kara kaimi wurin kai hare-hare ta sama a yankin."

Hafsan rundunar ya ba da umarnin kakkabe 'yan bindiga a yankin

Sanarwar ta kara da cewa:

"A karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara, rundunar ta kashe mayaka 16 a maboyarsu da ke biyayya ga kasurgumin dan bindiga da ake kira Dankarami.
"An kai samamen ne bayan samun bayanan sirri yadda Dankarami ke addabar mutanen yankin a karamar hukumar Zurmi.
"Har ila yau, rundunar ta kai hari maboyar 'yan bindiga da ke biyayya ga Aliero a dutsen Asola da ke karamar hukumar Tsafe a jihar bayan samun bayanan sirri.
"Ana zargin su ne da cewa shanu a kwanakin nan a kananan hukumomin Tsafe da Faskari ta jihar Katsina."

Kara karanta wannan

Kwana Daya Bayan Rushewar Masallaci, Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Zariya, Sun Sace Wani

Kakakin rundunar sojin saman, Edward Gabkwet ya fadawa 'yan jaridu cewa babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar ya umarci ci gaba da kakkabe 'yan bindigan a yankin, cewar Vanguard.

Yan Bindiga Sun Sace Mutum 13 A Wani Sabon Hari A Zamfara

A wani labarin, 'yan bindiga sun sake kai hari a jihar Zamfara tare da sace mutane uku.

'Yan bindigan yayin harin sun hallaka mutane uku a kauyen Mayanchi da ke karamar hukumar Maru a jihar.

Harin na zuwa ne bayan tsageru sun sace mata 23 da wasu ma'aikatan kananan hukumomin Maradun da Talata Mafara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.