Bayan Shekaru 8, Abba Gida Gida Zai Karasa Aikin da Kwankwaso Ya Bari a Kano
- Abba Kabir Yusuf ya duba aikin titin Wuju-Wuju, ya dauki alkawarin kammala bangaren hanyar
- Bayan dawowa daga wata tafiya, Gwamnan jihar Kano da wasu Kwamishinoninsa sun duba kwangilar
- Ibrahim Dala shi ne wanda aka nada ya zama Kwamishinan bibiyar ayyuka da tabbatar da nagarta
Kano – A farkon makon nan, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kai ziyara ta musamman domin duba aikin babban titin Wuju-Wuju.
Kamar yadda ya sanar a shafin Facebook a ranar Talata, Mai girma Gwamnan ya ce za su yi kokarin kammala aikin kafin ya kwana 100 a ofis.
Abba Kabir Yusuf zai cika kwana 100 a kan mulki ne a farkon watan Satumba mai zuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jawabin Abba Kabir Yusuf
"A yau na kaddamar da aikin titin Wuju Wuju.
Wannan titi mai tsawon kilomita 6.47 wanda ya hada da hanyar ruwa ya hada da madatsan Minjibir wanda gwamnatin Kwankwaso ta fara.
Idan Allah ya so, gwamnatinmu za ta karasa wannan aiki. – Abba Kabir Yusuf."
Saura kwanaki kusan 40
Mai taimakawa Gwamnan a kafofin zamani, Salisu Yahaya Hotoro ya fitar da sanarwa, yana mai tabbatar da za a kammala aikin a Satumba.
Hotoro ya ce Kwamishinoni biyu su ka yi wa Gwamna Abba rakiya zuwa wajen duba aikin.
“A yammacin talata mai girma gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar duba aikin babban titin Wuju-Wuju dake cikin birnin Kano.
Yayin duba aikin mai girma gwamnan yayi alƙawarin kammala wani babban kaso daga cikin aikin tare da buɗe shi kafin cikar sa kwanaki 100 a mulki.
Yayin ziyarar mai girma gwamna yana tare da Kwamishinan ayyuka na jihar Kano Engr. Marwan Ahmad tare da Kwamishinan bibiyar ayyuka da tabbatar da nagartar su Hon. Ibrahim Namadi Dala.”
- Salisu Yahaya Hotoro
Gwamnoni na kawo tallafi iri-iri
A rahotonmu na jiya, an ji Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda ya bada umarnin fito da buhuna 36, 100 na hatsi domin a rabawa mutane.
Za a fito da kayan abincin ne domin rabawa talakawan da ke duka kananan hukumomin jihar sakamakon matsin lambar da ake ciki.
Asali: Legit.ng