Atiku Zai Halarci Zaman Kotun Da Za A Yi Yau Don Gabatar Da Kuduri Na Karshe
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zai halarci zaman kotu a yau Talata
- Atiku na kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a watan Fabrairu na wannan shekara
- Atiku zai gabatar da korafe-korafensa na karshe da suka hada da zargin safarar miyagun kwayoyi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zai halarci zaman kotun sauraran kararrakin zabe a yau Talata 1 ga watan Agusta a Abuja.
Atiku zai karanto tuhumarsa ta karshe da suka hada da zargin safarar kwaya na Shugaba Bola Tinubu.
Bayan karanto dukkan zarge-zargen da dama suna gaban kotun, akwai yiyuwar kotun ta sake saka ranar ci gaba da sauraran karar ko kuma ta yi watsi da karar.
Korafe-korafen da Atiku ya gabatar a gaban kotun
Korafe-korafen sun hada da mallakar takardun kasancewa dan kasashe biyu da ke haramta masa zama shugaban Najeriya, Legit.ng ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mallakar shaidan kasancewa dan kasashe biyu ya sabawa dokar zabe da aka mata gyaran fuska a shekarar 2022.
Ana zargin Shugaba Bola Tinubu da mallakar takardan shaidan zama dan kasar Guinea da ke Nahiyar Afirka, Channels TV ta tattaro.
Bayan zarge-zarge akan safarar kwayoyi da ake a kansa, akwai zargin tafka magudin zabe da aka gudanar a watan Fabrairu na wannan shekara
'Yan takarar da ke kalubalantar zaben Tinubu
Sauran korafe-korafen sun hada da wasu matsaloli na Tinubu da ka iya hana shi zama halastaccen shugaban kasa.
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi shi ma na daga cikin masu kalubalantar sahihancin zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Bola Tinubu ya tsaya takara ne a jam'iyyar APC mai mulki, inda yayin rantsar da shi a watan Mayu ya nemi hadin kan sauran 'yan takara don ci gaban kasa.
Kotu Ta Amince Da Korafin Atiku Kan Tinubu Dangane Da Jami'ar Chicago Da Shaidar Yin NYSC
A wani labarin, kotu ta karbi korafin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar kan zargin Tinubu.
Atiku na kalubalantar Bola Tinubu kan shaidar yin bautar kasa da kuma ikirarin yin jami'ar Chicago.
Kotun ta karbi wannan takardun da suka hada da takardar shaidar bautar kasa da na kammala digiri da kuma takardar shaidar aiki na kamfanin Mobil Oil.
Asali: Legit.ng