Fastoci Sun Gargadi Tinubu Kan Tsarin Cire Tallafi, Sun Ce Kasar Na Daf Da Rugujewa

Fastoci Sun Gargadi Tinubu Kan Tsarin Cire Tallafi, Sun Ce Kasar Na Daf Da Rugujewa

  • Kungiyar Limaman Majami'u a Najeriya, CBCN ta soki tsarin ba da tallafi da gwamnati ta shirya bayarwa
  • Kungiyar ta ce Najeriya na daf da rugujewa idan ba a sauya tsarin shawo kan matsalolin da kasar ke fama da su ba
  • Shugaban kungiyar, Lucius Ugorji shi ya bayyana haka a birnin Owerri na jihar Imo a jiya Lahadi 30 ga watan Yuli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Gamayyar Fastocin Majami'a a Najeriya (CBCN) sun koka kan yadda cire tallafin mai ke neman ruguza Najeriya.

Kungiyar ta bayyana cewa rashin tsari mai kyau na rage radadin cire tallafi ba karamin hatsari ba ne ga kasar baki daya.

Fastoci a Najetia sun ce kasar na daf da rugujewa idan ba a dauki mataki ba kan cire tallafi
Gamayyar Fastocin Sun Gargadi Tinubu Kan Tsarin Cire Tallafi Ba Tare Da Daukar Matakin Rage Radadi Ba. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Shugaban gamayyar, Rabaran Lucius Iwejuru Ugorji shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 30 ga watan Yuli a birnin Owerri na jihar Imo, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Akwai sharrin Turawa: Shehu Sani ya fadi abubuwa 5 da suke sa juyin mulki a Afrika

Ya ce Najeriya na daf da rugujewa akan cire tallafin mai

Ya ce Najeriya na daf da rugujewa idan har Gwamnatin Tarayya ba ta samar da wani yanayi ba da zai shawo kan wadannan matsaloli, Premium Times ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Wahalhalun da kullum 'yan Najeriya ke ciki karuwa su ke ba tare da an iya shawo kan matsalar ba.
"Matsalolin sun karu tun bayan cire tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ke neman jefa kasar cikin mayuyacin hali.

Ya bayyana yadda gwamnati ke yaudarar mutane da kudin tallafi

Ya kara da cewa:

"Gwamnatin ta ci gaba da yaudarar mutane akan tallafin da ba shi da tabbas da kuma wadatar mutane.
"Na tabbatar masu rike da madafun iko a ko wane mataki sun san wannan tallafi babu abin da zai rage na matsalolin tattalin arziki da lafiya."

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: An Bayyana Mutanen Da Shugaba Tinubu Zai Naɗa a Matsayin Ministoci Kwanan Nan

Lucius ya ce meye amfanin ba da tallafin abinci da aka san bayan ya kare za a sake shiga yunwa? ya ce dole a shawo kan matsalar kasar daga tushe, cewar Ripples Nigeria.

Cire Tallafi: Kwamitin Rabon Kayan Tallafi Na Tinubu Ya Gana A Abuja

A wani labarin, Kwamitin rabon kayan tallafi na Shugaba Tinubu ya gudanar da ganawa ta musamman a ranar Asabar 15 ga watan Yuli.

Daga cikin mahalarta taron akwai gwamnonin jihohin Bauchi da Benue da Anambra da Kaduna.

Har ila yau, wakilan Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC su ma sun samu wakiltar kungiyar a ganawar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.