Gwamnan Adamawa Fintiri Ya Dura Bauchi, Ya Nemi Gwamna Bala Ya Saki Sheikh Idris Abdulaziz

Gwamnan Adamawa Fintiri Ya Dura Bauchi, Ya Nemi Gwamna Bala Ya Saki Sheikh Idris Abdulaziz

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an sasanta tsakanin gwamnan jihar Bauchi da Sheikh Idris Abdulaziz
  • An ce gwamnan jihar Adamawa ne ya jagoranci malamai don ganawa da gwamna Bala Muhammadu an jihar Bauchi
  • A baya an bayyana abin da ya faru har aka tsare malamin addinin a magarkama saboda wasu kalaman maras dadi

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya jagoranci manyan malamai na kungiyar Izala zuwa Bauchi domin nemawa Sheikh Idris Abdulaziz sauki a shari’ar da ake ta zarginsa da tayar da hankalin jama’a.

Fintiri tare da shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau da sakatarenta Sheikh Kabiru Gombe da kuma wani malami mazaunin Kano Sheikh Abdulwahhab sun gana da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad.

An roki gwamnan Bauchi ya yafe wa Dr Idris
Lokacin da aka je roka wa Dr Idris alfarma | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sun zo don nuna kokarinsu na ganin sun taimaka gwamnan ya janye tuhumar da gwamnati ke yi wa Sheikh Idris Abdulaziz, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Malaman Addinin Musulunci a Arewa Sun Roki a Hana El-Rufai Yin Minista, Sun Bayyana Dalili

Abin da ya faru na sasanta Sheikh Idris da gwamnan Bauchi

Babban sakataren yada labarai na Fintiri, Humwashi Wonosikou, ya tabbatar wa majiya ganawar, inda ya ce gwamnan ya gana da takwaransa na Bauchi domin sasanta al’amarin tsakanin gwamnatin Bauchi da Sheikh Idris.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sheikh Idris, wanda aka sake a ranan ya kasance a gidan yari sama da kwanaki talatin bayan da alkalin kotun shari’a da ke sauraron karar ya ba da umarnin a ci gaba da tsare shi.

Abin da ake zargin Sheikh Idris da aikatawa

Malamin dai ya yi wasu kalamai ne akan Annabi Muhammad SAW da wasu malamai da dama ke kallon su a matsayin cin mutuncin ga ma’aiki, inda shi kuwa ya musanta aikata ba daidai ba.

Wani malami a Kano, Baffa Hotoro wanda ya goyi bayan Sheikh Idris ya shiga hannun jami’an tsaron farin kaya (DSS) a Kano saboda ya maimaita kalaman Sheikh Idris

Kara karanta wannan

Mu je zuwa: Tinubu ya nada fitaccen masani don yin bincike a lamurran CBN

A gefe guda, wasu ’yan daba sun kashe wani mutum kwanan nan a Sokoto bisa zarginsa da irin wadannan kalamai na Sheikh Idris.

Sai dai, wasu na ganin akwai ‘yar tsama a tsakanin gwamnan na jihar Bauchi da Sheikh Idris, wanda aka ce hakan ne ya jawo tsare shi.

Malam Idris Zai Ci Gaba da Zamaan Gidan Kaso Saboda Dalilai Na Beli

A wani labarin, fitaccen malamin addinin Islama a Bauchi, Dakta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, zai ci gaba da zaman gidan dan kande bayan sake jinkirta belinsa saboda wani tsaiko.

A ranar Laraba ne kotun ta sake zamanta bayan shafe kwanaki 30 tana tsare da malamin a gidan yarin Bauchi.

Lauyoyin wanda ake tuhuma karkashin jagorancin Barista Abubakar Sadiq, sun shaida cewa kotun ba ta da hurumin ci gaba da zaman shari’ar kasancewar an dage karar zuwa babbar kotun tarayya ta 7 da ke Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.