Hukumar DSS ta saki shahararren Malamin Musulunci na Bauchi da ta tsare

Hukumar DSS ta saki shahararren Malamin Musulunci na Bauchi da ta tsare

Rundunar tsaro na sirri (DSS) ta saki shahararren malamin nan, Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi wanda ta tsare bayan ya amsa wasu yan tambayoyi da tayi masa.

Malam Abdulaziz wanda ya kasance babban limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, ya shiga hannun DSS ne a ranar Juma’ar da ta gabata.

Daya daga cikin mambobin majalisar daliban malamain, Muhammad Abdulkadir ya tabbatar das akin Malamin nasu a yau Juma’a, 17 ga watan Mayu.

Ya kara da cewa, wannan kamun da aka yi wa Malaminsu zai kara masa daukake ne ma a idon duniya ba kuma tauye masa kimarsa ba.

Hukumar DSS ta saki shahararren Malamin Musulunci na Bauchi da ta tsare
Hukumar DSS ta saki shahararren Malamin Musulunci na Bauchi da ta tsare
Source: UGC

Muhammad Abdulkadir ya bayyana cewar zuwa yanzu dai ba su da wata masaniya kan ko hukumar tsaron ta gindaya wa Malaminsu wasu sharuda, ya dai tabbatar da cewar an sako shi kuma ya dawo cikin iyalansa lafiya ba tare da wani matsala ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Kaduna ta amince da N54m don zabu sabbin ayyukan ci gaba a karamar hukumar Kaura

A baya mun ji cewa, hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta yi ram da wasu manyan Malaman addinin Musulunci a jahohin Katsina da Bauchi, Sheikh Aminu Usman inkiya Abu Ammar da kuma Ustaz Idris Abdulaziz biyo bayan gayyatar da hukumar tayi musu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kimanin kwanaki biyar da suka gabata ne hukumar DSS ta gayyaci Ustza Idris zuwa ofishinta dake jahar Bauchi domin amsa wasu tambayoyi, sai dai daga nan kuma suka yi awon gaba dashi zuwa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da yi masa tambayoyi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel