Tinubu Ya Nada Mai Bincike Na Musamman Domin Bincikar CBN Na Tsaka da Shari’ar Emefiele

Tinubu Ya Nada Mai Bincike Na Musamman Domin Bincikar CBN Na Tsaka da Shari’ar Emefiele

  • Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya sanar da fara bincike kan babban bankin CBN da sauran wurare
  • An dauki mai bincike na musamman da zai yi aikin, kuma zai ba shugaban kasa rahoton bincike kai tsaye
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da tsare tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele saboda wasu dalilai

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na Najeriya ya nada wani jami’in bincike na musamman da zai binciki Babban Bankin Najeriya (CBN) da wasu hukumomi masu alaka da shi.

A wata wasika da majiya ta gani, shugaban ya bayyana Jim Osayande Obazee, babban jami’in Hukumar ba da Rahoton Kudi ta Najeriya (FRCN), a matsayin mai binciken.

Shugaban kasar ya bukaci mai binciken na musamman da ya binciki CBN da manyan Kamfanonin Kasuwancin Gwamnati (GBEs).

Kara karanta wannan

Bidiyon Tinubu Yana Rokon El-Rufai a Fili, Ya Karbi Mukami Idan An Kafa Gwamnati

Tinubu ya nada wanda zai binciki CBN
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ina za a kai rahoton binciken CBN?

Ya kuma ce Obazee zai kai rahoton duk abin da ya samu zuwa ofishinsa kai tsaye, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar wasikar, daidai da sashe na 15(5) na kundin tsarin mulkin kasar, gwamnatin Tinubu ta ci gaba da aikin yaki da rashawa yadda ya dace.

Shugaban ya kuma aike da kwafin umarninsa na tsige Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin CBN a ranar 9 ga Yuni, 2023 hade wasikar binciken.

Tsohon gwamna Emefiele a hannun DSS

Tun lokacin dai Emefiele ke hannun DSS. A makon da ya gabata ne aka gurfanar da shi a gaban kotu inda aka ba da belinsa amma rundunar DSS ta sake kama shi.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da cece-kuce da ta’ajibin abin da ya faru tsakanin jami’an gidan yari da kuma na DSS a wajen kotun Ikoyi. Legas.

Kara karanta wannan

Ganduje da Tsofaffin Gwamnoni 7 da Tinubu Ya Watsar Wajen Rabon Mukaman Minista

A tun farko, an kama Emefiele ne bisa zarginsa da saba doka jim kadan bayan da aka sanar da tsige shi a kujerarsa.

Dalilin rigima tsakanin DSS da jami'an gidan yari a kotu kan Emefiele

A wani labarin, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce za ta gudanar da bincike kan rikicin da ya barke tsakanin jami’anta da na hukumar gidan yari (NCoS) a babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a ranar 25 ga watan Yuli.

A ranar Talata ne Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya gurfana a gaban babbar kotun kuma Alkali ya bayar da belinnsa kan N20m.

Mai shari'a Nicholas Oweibo, ya yanke hukuncin cewa a ci gaba da tsare Emefiele a gidan gyaran hali, har sai an cika sharuddan belinsa amma jami’an DSS suka dage sai sun tafi da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.