Abba Kabir Ya Fara Bincike Akan Karkatar Da Makudan Kudade Har Biliyan 4 A Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta fara binciken wasu makudan kudade da aka neme su aka rasa a wata hukuma a jihar
- Hukumar Yaki da Cin Hanci a jihar, PCACC ita ke binciken batan kudaden a hukumar Samar da Kayan Noma ta KASCO
- Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji ya ce suna zargin hukumar KASCO ta karkatar da kudaden ta wata hanya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Hukumar Yaki da Cin Hanci (PCACC) a jihar Kano ta fara binciken wasu makudan kudade har Naira biliyan 4 da suka bace.
Hukumar na zargin batan kudaden ne a Hukumar Samar da Kayan Noma (KASCO) ba tare yin bayanin yadda kudaden suka bace ba.
Muhuyi ya bayyana yadda aka karkatar da kudaden a Kano
Shugaban hukumar, Magaji Muhuyi Rimingado shi ya bayyana haka yayin rangadi a ma'ajiyar hukumar Pulse ta tattaro.
Cire Tallafin Mai: Jihohin Arewa Ne Suka Fi Shiga Matsi Kamar Yadda Sabbin Alkalluma Suka Nuna, An Ba Da Bahasi
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce ya je ma'ajiyar hukumar ne da ake zargin an adana motoci da taraktan noma da sauran kayayyaki da aka siya da kudaden a karamar hukumar Kumbotso.
Ya kara da cewa ana zargin hukumar KASCO ta tura kudin ga wata kungiya mai suna 'Association of Compassionate Friends'.
A cewarsa:
"Kungiyar an kirkire ta ne don kula da yara marasa karfi a al'umma, amma abin takaici sun koma satar dukiyoyin jama'a."
Muhuyi ya ce gwamnatin jihar Kano ce ta samar da kudaden a matsayin tallafi ga KASCO amma kuma aka karkatar da kudaden zuwa wata kungiya, cewar Daily Post.
Ya ce hukumar ta kama mutane 8 da kuma tarun kudade
Ya ce:
"A yanzu haka mun kama wadanda ake zargi su takwas inda suke ba mu bayanai masu muhimmanci.
"Daya daga cikinsu ya ce an ba shi wani kaso na kudin amma bai taba su ba saboda gudun rana irin haka, ya kuma dawo da kudin.
"A yanzu haka mun samu Naira miliyan 15 kuma munyi nasarar tare Naira miliyan 8 daga turasu wani asusun banki."
Rimingado ya ce hukumar na zargin hada-hadar kudade tsakanin kamfanoni da bankuna.
Ya ce watakila za su gayyaci manajojin banki su zo don fayyace wasu abubuwa, Independent ta tattaro.
Kano: Rimingado Ya Sha Alwashin Ci Gaba Da Binciken Badakalar Ganduje Akan Daloli
A wani labarin, shugaban hukumar yaki da cin hanci a jihar Kano, Muhuyi Magaji ya sha alwashin ci gaba da binciken bidiyon dala.
Rimingado ya ce hukumar za ta binciki bidiyon dala da aka gano tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje na yi.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Gwamna Abba Gida Gida ya dawo da Muhuyi kujerarsa a ranar 21 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng