'Yan Bindiga Sun Sace 'Yan Mata 23, Bayan Yin Garkuwa Da Ma'aikatan Kamfanin Hanya 10 A Zamfara

'Yan Bindiga Sun Sace 'Yan Mata 23, Bayan Yin Garkuwa Da Ma'aikatan Kamfanin Hanya 10 A Zamfara

  • Tsageru sun sace wasu mata 23 a kauyen Damagu da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara
  • 'Yan bindigan sun yi wa matan kwanton bauna ne yayin da suke dibar itace a daji inda tsageran suka far musu tare da kwashe su
  • Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yazid Abubakar ya cI tura saboda rashin samun wayarsa

Jihar Zamfara - Akalla mata 23 ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Damagu da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Matan an sace su ne lokacin da suke diban itacen girki a ranar Laraba 26 ga watan Yuli inda 'yan bindigan suka far musu a kan babura, Daily Trust ta tattaro.

'Yan bindiga sun sace mata 23 da wasu ma'aikatan kamfani 10 a jihar Zamfara
Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace 'Yan Mata 23 A Wani Hari A Jihar Zamfara. Hoto: BBC.
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin, Muhammad Sani ya fadawa Punch cewa tsageran sun fito daga cikin daji ne tare da kwashe matan zuwa sansaninsu.

Kara karanta wannan

Hankula Sun Tashi Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Bindige Wasu Dalibai A Shagon Aski, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Matan suna diban itace a bakin daji, kwatsam sai ga 'yan bindigan sun fito sai suka kwashe su zuwa sansaninsu.
"Mun riga mun sanar da 'yan sanda yanzu muna jira mu ji daga bakin 'yan bindigan ne nawa za su ce a biya kudin fansa."

'Yan bindigan sun kuma sace ma'aikatan kamfani 10

Sani ya koka kan yadda garkuwa da mutane ya yi yawa inda ya ce a kullum cikin biyan kudin fansa suke yi.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yazid Abubakar ya ci tura saboda rashin samun wayarsa har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Har ila yau, 'yan bindiga sun sace wasu ma'aikata 10 na kamfanin yin hanya na Triacta a Talata-Mafara.

Isma'il Shehu, wani mazaunin yankin ya tabbatar cewa tsageran sun yi ta harbi sama kafin daga bisani su kutsa da karfi cikin kamfanin tare da sace ma'aikatan 10, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji Da Manoma A Jihar Zamfara

A wani labarin, 'yan bindiga sun kai hari tare da kashe sojoji bakwai da wasu manoma 22 a jihar Zamfara.

Wannan hari ya faru ne a kauyen Kangon Garucci a yankin Dangulbi da ke karamar hukumar Maru.

Wasu mazauna yankin sun ce harin ya rutsa da wasu a gonakinsu yayin da wasu kuma musayar wutan ne ta rutsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.