Malaman Musulunci Sun Soma Jan Hankalin Gwamnatin Tinubu Kan Tsadar Rayuwa
- Farfesa Ibrahim Maqari ya yi maganganu a dalilin tashin farashin man fetur da aka yi a Najeriya
- Babban limamin ya ce dole a kara albashi, kuma ya bada shawarar mutane su taimakawa juna
- Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi wa’azi a game da muhimmancin komawa Allah a lokacin tsanani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Halin da jama’a su ka samu kan su na tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya a kasuwa, ya jawo mutane da-dama su na kokawa.
Abin ya kai wasu malaman addinin musulunci su na tofa albarkacin bakinsu, su na bada shawarwaru a matsayinsu na jagororin al’umma.
Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari ya fitar da gajeren jawabi a shafinsa na Twitter a karshen makon jiya, ya ce ya kamata a tausaya talakawa.
A saukakawa mutane zirga-zirga
Limamin babban masallacin Abuja ya ce wajibi ne samar da hanyoyin zirga-zirga cikin sauki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Hukumomi su gaggauta samarwa talakawa isassun motocin sufuri, don zirga zirgansu cikin rahusa, hakki ne ba alfarma ba.
Mai abin hawa, ya ragewa marasa hali hanya, sadaka ce da ba za ta rage shi da komai ba.
Tafiya bisa keke ko da kafa idan waje bai gagara ba, ni'ima ce ba alamar gajiyawa ba.
- Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari
Za a kara albashin ma'aikata?
A wani karatu da ya yi, Legit.ng Hausa ta ji shehin yana jimamin yadda farasin cika tankin mota da fetur ya zarce albashin wasu ma’aikata.
Sheikh Maqari ya ce hankali ba zai dauka ba a ce za a bar ma’aikata ba tare da an yi masu karin albashi ba, ganin yadda man fetur ya yi tsada.
Da yake rufe wani karatunsa, Sheikh Adamu Dokoro ya nuna damuwarsa ga tsare-tsaren da gwamnatin sabon shugaba Bola Tinubu ta kawo.
Jagaban ya yi gaba!
“Jagaba ya ja gaba, kwarai da gaske, ya ja ya yi gaba, to ba mu san kuma mu da ya bar mu a baya, ya za ayi ba.
Ba mu san yadda za ayi da wannan tsadar rayuwa ba, saboda haka mu na rokon Allah SWT ya kawo mana sauki.”
- Sheikh Adamu Muhammad Dokoro
A komawa Allah (SWT)
A yayin da yake amsa tambayoyi a shirin fatawowin Rahma a ranar Asabar, Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi kira da a komawa Allah (SWT).
Rijiyar Lemu ya nuna muddin mutane ba su komawa Ubangiji ba, ba za su ga canjin kirki ba, kuma kullum za a rika cewa jiya ta fi yau kyau.
Meyasa aka cire tallafin fetur?
An rahoto Gwamnan Ogun yana cewa a dalilin tsarin tallafin fetur, gwamnatin tarayya ta na rasa Naira tiriliyan hudu a kowace shekara.
Dapo Abiodun ya ce Shugaban kasa bai bari an kawo matakan rage radadin kafin kawo tsarin ba ne domin ya san mugun halin 'yan Najeriya.
Asali: Legit.ng