CBN Ya Yi Karin Haske Kan Makomar N200, N500 da N1000 da Aka Kori Emefiele

CBN Ya Yi Karin Haske Kan Makomar N200, N500 da N1000 da Aka Kori Emefiele

  • Gwamnan rikon kwarya na CBN ya yi magana a kan canjin takardun kudi da aka fara a Najeriya
  • Folashodun Shonubi ya ce idan tsofaffin kudi sun shigo hannunsu, ana canza su ne da sababbi
  • Nan da wani lokaci, babban bankin yake sa ran za a daina ganin tsofaffin N200, N500 da N1000

Abuja - Babban bankin Najeriya na CBN, ya ce a hankali-a hankali za a cigaba da janye takardun kudin N200, N500 da kuma N1, 000.

Yayin da ake cigaba da buga sababbin kudin da aka kawo, Gwamnan rikon kwarya na CBN, The Cable ta ce ya yi maganar yadda ake ciki.

Folashodun Shonubi ya samu damar yi wa manema labarai bayani a bankin CBN a Abuja bayan an tashi daga taron MPC a ranar Talata.

Kara karanta wannan

CBN Ya Bude Asusun Mutane da Kamfanoni 440 da Aka Rufe da Aka yi Canjin Gwamnati

CBN: An yi taron MPC a Abuja

Da yake bayanin inda aka kwana a yau, Folashodun Shonubi ya shaida cewa CBN ya su na canzawa bankuna tsofaffin kudin da sababbinsu

A maimakon ayi ta fitar da sababbin kudi, gwamnan rikon kwaryan ya ce CBN na bari sai tsofaffin kudi ya shigo hannunsu, sai a canza su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban bankin Najeriya
CBN: Godwin Emefiele a lokacin yana Babban bankin Najeriya Hoto: @cenbank
Asali: Twitter

Bayanin Folashodun Shonubi

"Idan aka buga sabon kudi aka fitar da shi. Ana sa ran zai dauki wani tsawon lokaci, bayan nan za a maye gurbinsa, haka mu ke yi.
Dole mu janye tsofaffin kudi. Yayin da su ke dawo mana, mu na karbe su domin a daina amfani da su, sai mu canza su da sababbin kudi.
Mun gamsu mu na da isassun takardun kudi, akasari abin da mu ke yi shi ne maye gurbinsu domin mu iya rika adadin da ake da shi.

Kara karanta wannan

‘Dan Wasan Super Eagles, Ahmed Musa Ya Karya Man Fetur, Lita Ta Koma N580 a Kano

Duk lokacin da bankuna su ka zo wurinmu karbar kudi, mu na ba su. Idan babu yawa, za su nemi kari, idan yayi yawa, sai a bar mu da su."

- Folashodun Shonubi

Tsofaffin kudi za su bace nan gaba

Kamar yadda rahoton Punch ya nuna, Shonubi yana mai sa rai bayan wani lokaci za a nemi tsofaffin kudin a rasa, sababbin sun cika ko ina.

Sannu a hankali za a cin ma hakan, ba kwatsam za a nemi tsofaffin kudin a rasa ba.

Fito da tsarin canza kudi

Za a tuna cewa a 2022 ne Godwin Emefiele a lokacin yana Gwamnan babban banki na kasa ya sanar da Duniya cewa za ayi canjin kudi.

Canjin ya shafi takardun N200, N500 da N1,000 wanda a karshe Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adinsu, kafin kotun koli tayi hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng