Sanatoci Sun Bukaci Oshiomole Ya Nemi Afuwa Bisa Zargin Sata Da Ya Yi Musu

Sanatoci Sun Bukaci Oshiomole Ya Nemi Afuwa Bisa Zargin Sata Da Ya Yi Musu

  • Sanatoci musamman waɗanda suka yi zama a majalisa ta tara sun fusata kan kalaman da Oshiomole ya yi na zarginsu da sata
  • Sanatocin sun bayyana cewa Oshiomole ya taɓa musu ƙimarsu inda suka buƙaci da ya nemi afuwa a gaban majalisar
  • Oshiomole ya nemi afuwa bisa kalaman nasa da ya yi inda ya bayyana cewa ba a fahimce shi ba ne gaba ɗaya

FCT, Abuja - Wasu Sanatoci musamman waɗanda suka kasance a majalisa ta tara, sun buƙaci Sanata Adam Oshiomole ya nemi afuwa bisa zargin sama da faɗi da kayayyakin majalisa.

Oshiomhole, a wata hira da gidan talbijin na Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' ranar Lahadi, ya yi zargin cewa Sanatoci da ƴan majalisar wakilai na majalisa ta tara, sun yi awon gaba da kayayyakin dake cikin ofisoshinsu.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Mutane Sama da 100 Kan Zargin Aika Muggan Laifuka Daban-Daban a Arewa

Sanatoci sun bukaci Oshiomole ya nemi afuwa
Sanatocin basu ji dadin kalaman Oshiomole ba Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa da yawa daga cikin ƴan majalisun da aka zaɓa a majalisa ta 10 da kuɗin aljihunsu suka yi amfani wajen gyara ofisoshinsu.

Sai dai, a zaman majalisar na ranar Talata, Sanata Adeola Solomon (APC Ogun ta Yamma), ya gabatar da ƙudiri yana neman Oshiomole da ya nemi afuwa kan kalamansa, cewar rahoton The Punch.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya yi nuni da cewa kalaman na Oshiomole cin mutunci ne ga ƴan majalisar sannan an taɓa masa ƙimarsa.

A kalamansa:

"An ci min zarafin ƙimata. Sanatan Najeriya ya je gidan talabijin ya gayawa duniya cewa ƴan majalisun majalisa ta tara, wanda ina ɗaya daga cikinsu, sun sace kayayyaki daga ofisoshinsu."
"Mun sani cewa babu yadda za a yi Sanata ko hadimansa su ɗauki ko da tsinke ne a majalisar ba tare da an gano su ba."

Kara karanta wannan

Oshiomole Ya Ce N30,000 Ta Yi Kadan Matsayin Albashi, Ya Bayyana Ainihin Yadda Ya Kamata a Riƙa biya

"Kowane daga cikin kayayyakin nan sai an duba su da amincewa da su sannan waɗanda basu a cire kuɗinsu daga cikin alawus na ƴan majalisu."
"Saboda haka ina neman Sanatan ya nemi afuwa ga majalisa ko a sanya shi ya fuskanci kwamitin ɗa'a."

Sanata Abdullahi Adamu Aliero (PDP Kebbi ta Tsakiya) ya goyi bayan wannan kuɗirin da Sanata Adeola ya kawo gaban majalisar.

Ba a fahimce ni ba ne - Oshiomole

Oshiomole bayan an ba shi damar ya kare kansa, ya bayyana cewa ba cewa ya yi Sanatocin sun sace kayayyakkin ofishinsu ba, face an lalata ofisoshin wanda hakan ya sanya Sanatocin yin amfani da kuɗinsu wajen gyara ofisoshin.

Sai dai, ya nemi afuwa ga Sanatocin da suka ce kalaman nasa basu ji daɗinsu ba, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Rabon Kwamitoci Ya Tayar Da Yamutsi a Majalisa

A wani labarin kuma, rabon kwamitoci a majalisar wakilai zai tayar da ƙura saboda yadda wasu ƴan majalisar suka fara ƙorafi an bar su a baya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bankaɗo Badaƙalar Maƙudan Kuɗi, Ya Ceto Biliyan N1.2 Daga Ma'aikata

Wasu daga cikin ƴan majalisar suna zargin cewa an fifita ƴan jihar Legas inda aka basu muƙamai a kwamitoci masu tsoka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng