Gwamnan Arewa Ya Karawa Duk Ma’aikacin Gwamnati Kudi a Dalilin Tsadar Man Fetur
- Gwamnatin Kwara ta fito da wasu tsare-tsare ganin an janye tsarin tallafin man fetur a Najeriya
- Abdulrahman Abdulrazaq ya amince a rika biyan ma’aikata N10, 000 kafin a kara masu albashi
- Gwamnan ya ce za a biya ma’aikatan asibiti alawus, a raba kayan abinci kuma a tallafawa ‘yan kasuwa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kwara - A dalilin halin da aka shiga ciki a yau, duk wani ma’aikacin gwamnatin jihar Kwara ya samu karin kudi ganin an janye tallafin man fetur.
A ranar Litinin,Gwamnan Kwara ya sanar a Twitter cewa an fito da tsare-tsaren da za su taimakawa jama’a, bayan a baya ya nemi rage kwanakin aiki.
Abdulrahman Abdulrazaq ya amince a kashe makudan miliyoyi a karkashin tsarin rage radadin tallafi a sakamakon tashin farashin man fetur a kasar.
Kwara ta karbi shawarar NEC
A wani jawabi da ya fitar a jiya, Mai girma Gwamnan ya ce kamar yadda majalisar NEC ta ba Jihohi shawara, ya amince da tsarin da zai rage radadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Gwamnan, a watan Yulin nan za a fara biyan ma’aikatan gwamnati kyautar N10, 000, za a cigaba da biyan kudin ne har sai an yi karin albashi.
Kokarin inganta kiwon lafiya
Abdulrahman Abdulrazaq ya amince a fara biyan alawus na shiga hadari da karin 100% na kudin da ake biyan Likitoci a tsarin albashin CONMESS.
Malaman jinya da ake aiki a Kwara za su ci moriyar wadannan sababbin alawus da aka kawo, Gwamnan ya ce manufar ita ce gyara harkar kiwon lafiya.
...da rabon abinci a gidaje
Bugu da kari, Tribune ta ce nan da ‘yan kwanaki za a fara rabon abinci ga marasa karfi, gwamnatin jihar Kwara za ta shiga gidajen da ke shan wahala.
A jawabin da ya fitar, Abdulrazaq ya nuna ba za ayi la’akari da siyasa wajen rabon kayan ba, ya ce za a hada kai da shugabannin gargajiya da malamai.
‘Yan kasuwa da kungiyoyi za su shiga cikin tsarin domin ganin an bada tallafin da ya dace.
A karkashin tsarin KWASSIP na inganta rayuwar marasa galihu, Gwamnatin Abdulrazaq za ta kashe N500m a tallafawa kananan ‘yan kasuwa.
Ana jiran nadin Ministoci
Rahoto ya zo cewa watakila yau a karanto takardar shugaban kasa a Majalisa, a ji wadanda ake so a ba Minista bayan kwanaki 56 ana jiran tsammani.
Tsofaffin Gwamnonin da su ka taka rawar gani a zaben 2023 sun kasa sun tsare a Aso Rock, domin an fahimci Bola Tinubu zai iya ba ‘yan adawa mukami.
Asali: Legit.ng