‘Dan Wasan Super Eagles, Ahmed Musa Ya Karya Man Fetur, Lita Ta Koma N580 a Kano
- Duk wanda zai saye fetur a gidan man MY CA 7 a Kano, ai samu ragwame a yau
- Ahmad Musa ya sanar da cewa a kan N580 ya saida lita, akasin N620 da ake saye
- Tauraron 'dan kwallon kafan ya tausayawa mutane, ganin irin halin da aka shiga
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - A lokacin da mutane su ke wayyo Allah da tsadar rayuwa, musamman farashin fetur, sai aka ji Ahmad Musa ya kawo sa’ida.
A yau Litinin aka ji samu labari ‘Dan wasan kwallon kafan Najeriya na Super Eagles, Ahmed Musa ya rage farashin man fetur a gidan mainsa.
Ga wadanda su ke zaune a garin Kano, za su iya zuwa gidan man ‘dan kwallon domin su sha fetur a kan N580, kasa da farashin gwamnati.
Maganar da mu ke yi, ana saida litar man fetur a mafi yawan gidajen man garuruwan Arewacin Najeriya ne tsakanin N617 da N620.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Musa ya bada sanarwa a shafinsa na Twitter cewa ya zabi ya karya farashin a gidan mansa da ke hanyar Zariya a unguwa uku a Kano.
“Fetur a kan #580 a gidan mai @MYCA - 7 a Kano.“
- Ahmad Musa
Wata miyar sai a makwabta
Tuni mutane su ka shiga yi wa ‘dan kwallon ruwan addu’o’i na wannan taimako da ya yi a sa’ilin da fetur ke neman ya gagari talakawa
Mazauna Legas sun yi mamakin irin wannan rahusa na tauraro kuma ‘dan kasuwan.
Wannan ya sa aka ji wata Salama Naziru ta na rokon ‘dan wasan ya taimakawa Gombawa da Sakkatawa da wannan rangwame na shi.
Masu bibiyar dandalin Twitter kuwa babu abin da su ke yi sai jinjinawa attajirin, ana yi masa addu’a Ubangiji ya kara masa dukiya mai yawa.
Abin da jama'a su ke fada
Engr. Fahad Shehu ya rubuta:
"Allah ya saka maka da alheri. Yayi ma rayuwar ka da ta iyalanka albarka. Allah ya jikan mahaifanka, Ya saka su aljannar firdausi. Amin Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum."
Wani Bawan Allah ya ce a kan N640 su ke sayen lita a gidajen mai. Kafin a iya cika tankin karamar mota, sai an kashe fiye da N30, 000.
Shi kuwa Malam Shehu Liman Bana ya ce su na alfahari da wannan Bawan Allah.
Motoci sun ragu a tituna
Al-Ameen Abbas mazaunin yankin ne, ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa ya sha mai kafin farashi ya tashi daga N540 zuwa N620 a makon jiya.
AYM Shafa su na cikin gidajen man da ba su yi gaggawar kara farashinsu ba.
Kamar yadda ya fada mana, kafin ayi karin kudin man, ana yawan samun cinkoso a tituna, abin da ya ce ya yi ragu sosai daga karshen Mayu.
Maganar Auwal Adam (Albani)
A wani tsohon karatu da Muhammad Auwal Adam Albani ya yi a lokacin rayuwarsa, an ji labarin yadda ya soki maganar janye tallafin fetur.
Marigayi Sheikh Auwal Albani ya ce su talakawan kasar nan ba su san fassarar cire tallafin ba, ya ce ba su san ma’anar shi ba, sai sun ji a jika.
Asali: Legit.ng