Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Gwamnan Enugu Peter Mbah Ya Mallaki Sabon Digiri a Jami’ar Oxford

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Gwamnan Enugu Peter Mbah Ya Mallaki Sabon Digiri a Jami’ar Oxford

  • Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya nuna farin cikinsa yayin da ya sanar da sabon ci gaban da ya samu a bangaren karatu
  • Mbah wanda ya garzaya shafinsa na soshiyal midiya a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli, ya bayyana cew ya mallaki sabon digiri a jami'ar Oxford da ke Landan
  • A halin da ake ciki, Mbah na a kotu kan ikirarin da hukumar bautar kasa ke yi na cewar ya kirkiri takardar shaidar kammala NYSC dinsa ne

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya sanar da cewar ya mallaki digiri a jami'ar Oxford da ke Landan.

Gwamna Mbah, ta shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli, ya bayyana cewa ya samu digiri a fannin Dabaru da kere-kere daga makarantar Said Business School na Jami’ar Oxford.

Kara karanta wannan

“A Wannan Marran”: Peter Obi Ya Yi Martani Ga Ma’aikaciyar Otel Da Ta Mayar Da Miliyan 55 Da Ta Tsinta

Gwamnan Enugu ya kammala digiri a jami'ar Oxford
Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Gwamnan Enugu Peter Mbah Ya Mallaki Sabon Digiri a Jami’ar Oxford Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Asali: Facebook

Gwamnan Enugu Peter Mbah ya mallaki sabon digiri a jami'ar Oxford, Landan

Wallafar wanda ke tattare da wani bidiyo ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yanzun nan na mallaki Digiri a fannin Dabaru da kere-kere daga makarantar Said Business School na Jami’ar Oxford, Oxford, kasar Ingili."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun taya gwamnan murnar wannan nasara da ya samu

Okechukwu Okafor ya yi martani:

"Na taya ka murna yallabai....Ina maka addu'an samun karin karramawa yallabai."

Elijah Nwaolisa Iyidaja ya rubuta:

"Ina taya ka murna mai girma gwamna."

Kennedy Nnaji ya ce:

"Ina taya ka murna yallabai."

Chuck Nnam ya ce:

"Okwute Enugu Nnoo!
"Na taya ka murna mai girma gwamna!
"Jihar Enugu za ta kara inganta!
"Shakka babu ga gobe ya zo."

Obiora Sampson Onyia ya yi martani:

"Na taya ka murna mai girma gwamnanmu. Shakka babu ka cancanci wannan karramawar."

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Farfesa Njodi a Matsayin SSG, Ya Kaddamar Da Kwamitin Masu Ba Shi Shawara

Dokar Zaman Gida: Muna Asarar Biliyan N10 Duk Ranar Litinin, Gwamna Mbah

A wani labarin kuma, Legit.ng ta kawo a baya cewa Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu, ya ce dokar zaman gidan da ƙungiyar 'yan aware IPOB ta ƙaƙaba a Kudu maso Gabas, tana jawa jiharsa asarar makudan kuɗaɗe.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa a kowace ranar Litini da dokar ke aiki, jihar Enugu na tafka asarar kuɗi kimanin biliyan N10bn, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng