Ku Ayyana Ni a Matsayin Shugaban Kasan Najeriya, Atiku Ya Fadawa Kotu a Jawabinsa Na Karshe
- Da alamu shugaban kasa Tinubu zai fuskanci damuwa kan shari’arsa da dan takarar shugaban kasa na PDP
- Ya zuwa yanzu, Atiu ya nemi a alanta shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya
- Atiku ya kafa hujjojin da ya ce shi ne ya lashe zaben, kana kotu bata musanta cewa shi ne ya ci zabe a jihohi 21 ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku, ya bukaci kotun sauraran kararrakin zabe da ta tabbatar da sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi cewa shi ne ya lashe jihohi 21 a zaben shugaban kasa da aka gudanar a bana.
Atiku ya yi wannan batu ne a ranar Juma’a a jawabinsa na karshe na kare kokensa na hadin gwiwa da jam’iyyar PDP na neman a soke alanta Ahmed Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, rahoton Daily Post.
A jawabin karshe da babban lauyansa Chris Uche SAN ya yi, Atiku ya bayyana cewa INEC ta ce shi ya ci zabe a jihohi 21, ba a yi jayayya ba, ko janye batun, ko ma karyata shi, ko kuma da’awar cewa kuskure ne a tsawon shari’ar kotun zuwa yanzu.
Martanin hukumar zabe ta INEC
INEC ta mayar da martani ga karar Atiku, inda ta ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya lashe jihohi 21 na tarayyar kasar a zaben shugaban kasa da ya gabata, Channels Tv ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jihohin 21 da INEC ta bayyana cewa Atiku da PDP sun lashe sun hada da Adamawa, Akwa Ibom Bauchi, Bayelsa, Borno, Delta, Ekiti, Gombe, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Osun, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tun da hukumar zaben ta yi ikirarin cewa shi ne ya lashe wadannan jihohin kuma ya yi fatali da hakan a duk zaman da ake a shari’ar, ya kamata kotun ta tabbatar da shi ne shugaban kasa.
Kotu ta amince da korafin Atiku kan Tinubu dangane da Jami'ar Chicago da shaidar yin NYSC
A wani labarin, kotun sauraran korafe-korafen zabe a Abuja ta amince da shaidar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar.
Kotun ta karbi wannan takardun ne a ranar Juma'a 23 ga watan Yuni da suka hada da takardar shaidar bautar kasa da na kammala digiri da kuma takardar shaidar aiki na kamfanin Mobil Oil Nigeria Plc.
Jam'iyyar PDP ta gabatar da shaidar ta hannun Mike Enahoro Ebah wanda ya ce takardun Tinubu ne ya karbe su amma suna dauke da sunan Bola Adekunle Tinubu, Daily Trust ta tattaro.
Asali: Legit.ng