Kano: Abba Gida Gida Ya Dakatar Da Shugabannin Makarantu 3 Saboda Rashin Kula Da Aiki
- Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare a karamar hukumar Dawakin Tofa
- Wadanda aka dakatar din ana zarginsu da rashin kula da kuma kin zuwa wurin aiki bayan wata ziyarar bazata
- Kwamishinan ma'aikatar ilimi a jihar, Umar Haruna Doguwa shi ya ba da umarnin a yau Juma'a 21 ga watan Yuli
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shugabannin makarantar sakandare uku saboda rashin zuwa wurin aiki.
Kwamishinan ilmi a jihar, Umar Haruna Doguwa shi ya ba da wannan umarni a yau Juma'a 21 ga watan Yuli.
Wadanda abin ya shafa sun hada da shugabannin makarantun sakandare na mata da G.A.S.S da ke Dawanau sai makarantar mata da ke Kwa duk a cikin karamar hukumar Dawakin Tofa, PM News ta tattaro.
Bidiyon Dala: Kungiya Ta Tada Jijiyar Wuya, Ta Ce Bai Kamata Tinubu Ya Ba Ganduje Da Doguwa Mukamai Ba
Dalilin dakatar da shugabannin makarantun uku
Kwamishinan ya dakatar da biyu daga cikinsu ne bayan ya ziyarci makarantar da misalin karfe 9 zuwa 10 na safe ba tare da ganin su ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar, Ameen Yassar ya sanya wa hannu ya ce biyu daga cikinsu sun ki zuwa aiki a ranar Juma'a na wasu lokuta, cewar Tribune.
Ya gargadi sauran ma'aikata akan aiki
A cewar sanarwar:
"Wannan gwamnati ba za ta amince da rashin zuwa aiki ba ko kuma zuwa ba a kan lokaci ba da kuma sauran halayyar da suka saba dokar aiki.
Kwamishinan ya umarci tura sabbi kuma kwararrun shugabanni a makarantun don ci gaba da karatu ba tare da tsayawa ba, cewar gidan talabijin na NTA.
Kwamishinan har ila yau, ya umarci ba da kyauta ga shugabar makarantar Harbau a karamar hukumar Tsanyawa saboda kokarin ta.
A Jira Lokaci: Abba Gida Gida Ya Magantu Kan Dawo Da Sarki Sanusi
A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa bai shirya dawo da Sarki Sunusi ba tukunna.
Gwamnan ya bayyana haka don kore jita-jitar da ake yadawa cewa ya na shirin dawo da tsohon sarkin.
Ya kuma bayyana cewa bai shirya wargaza masarautun da tsohon gwamna Ganduje ya yi ba.
Asali: Legit.ng